Connect with us

LABARAI

Gwamnan Nasarawa Ya Kasa Cika Alkawarin In ji Al’umman Jihar

Published

on

Gwamna Abdullahi Sule ya hau mulkin jihar Nasarawa a ranar Laraba 29/5/2019. Lokacin da aka rantsar dashi bai bar kan mumbarin rantsarwar ba yayi alkawarin cikin kwana dari zai kammala ayyukan da tsohon Gwamna Umar Tanko Al-makura ya fara bai karasa ba.
Gwamnan Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yayi bikin cika kwanaki dari a ranar Juma’a. Duk da cewa Gwamnan ya fara zagayen duba ayyukan ranar alhamis 5/9/2019. Amma yayi bikin ranar Juma’a 6/9/2019.
Wakilinmu ya zagaya guraren da tsohuwar Gwamnatin ta sanya ayyukan da bata kamala ba , kamar filin sauka da rashin jiragen Sama dake akwandare a garin Lafia. Da ayyukan tituna da suka hada daga mahadar titin tudun Gwadara zuwa mahadar Kilema .
Akwai ginannun dakunsn kwanan Dalubai wanda Gwamnatin ta gada kuma ba’a kamala ayyukan shiba bare Dalubai su tare. Kama daga kwalajin kimiyya da fasaha dake Lafia sai kwalajin koyon aikin Gona dake Lafia sai kwalajin Ilumi dake garin Akwanga.
Akwai ayyukan Gina Asibitin Dalhatu Araf wanda tsohuwar Gwamnatin ta ayikin yayi nisa amma Sabuwar Gwamnatin tace zata kamala.Akwai Asibitin Akwanga da makarantar kanasasu dake Gudi da sauransu.
Leadership A Yau Asabar ta tattauana da wasu jama’a an gari game da yadda suka ga ranar ayyukan Gwamnan cikin kwana 100.
Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa ai ma fi yawancin Gwamnoni ba ka iya gane ayyukan da suka yi cikin kwanaki dari, dole sai tafiya tayi nisa sanan.
Wani Marubuci , ya ce; alkawarin da Gwamnan ya yi wa al’umman jihar Nasarawa a gaskiya bai cika ba ya saba alkawarin.
Ya ce;ba komai ba ne ya kawo masa cikas cikin aikinsa face rashin kafa Kwamishinoni. Ya ce; duk Gwamnatin da ba ta yi Kwamishinoni ba akwai abubuwa da yawa da za su kawo cikas saboda akwai ayyukan da sai Kwamishinoni su ne za su ba da hankali akai.
Shi ma Malam Zurkallaini Isa ya ce Saraki goma zamani goma sukan Alhamdulillahi sun ga ci gaba a cikin wanan Gwamnati saboda a kwanki dari suna ganin canji.
Yanzu ana biyan Fanshoniya hakinsu dari bisa dari cikin alkawarin da yayi mana munga guda daya saboda haka muna fatan Allah yabashi ikon cika sauran.
Malam Yakubu Sulaiman mai sana’ar Buburutu a bakin titi ya yabawa Gwamnatin inda yake cewa ” mun yaba mada wanan Gwamnati a kwana dari ta kawar da damuwar ma’aikata suna karban albashi dari bisa dari kuma gashi ana tayin ayyukan titi a gari.”
Sanan ga matasa an basu injunan buga bulo zasuyi aiki surika samun kudi suna taimakawa iyalansu.
Kwamared Muhammad Abdul Keffi tsohon Shugaban kungiyar kwadagone ta jihar . kuma Dan fansho yace mudai bamugani a kasa ba saboda kudaden da nakebi a fansho haryau ba”‘abiyani ba dukda ance ana biya amma mu bamugani a kasa ba.
Gasjiya wanan da sake gara aduba ayi abin da ya kamata. Yanzu dai bamu gani ba ba mu san nan gaba ba.
Kuam da a ce Gwamnatin ta nada Kwamishinoni da akwai abubuwa dayawa da zasu taimaka masa .Amma hannu daya baya daukar jinka.
Muhammad Garba, yace agabana a filin taro Gwamnan yayi alkawarin zai kammala ayyukan tsohuwar Gwamnatin cikin kwana dari.
Amma mu dai da muke zaune a jihar Nasarawa bamu gani ba . yace a lokacin Gwamnatin baya a kwanaki Dari suna kadamar da ayyukan cigaba da sukayi amma wanan sabon Gwamnan bayi komai ba .
Kuma yayi yaunkurin karin girma ga ma’aikata amma abin takaichi sai ya dawo ya fasa haka akeson muyi tazama a waje daya kenan. Ku yan jarida kune abin da Gwamnati batayi ba sai abaku kudi kuna rubuta cewa anyi. Kuji tsoron Allah .
Itama Ester Godiya tace; batun karin girma da Gwamnan yayi yunkurin yi bai kamata ya fasaba . idan har ya fasa to gaskiya yaci amanar mutanin jihar Nasarawa. Saboda yayi alkawarin amma ya kasa cikawa.
A wani binciken da wakilinmu yayi game da yadda Gwamnatin jihar Nasarawa me tafiya tankar Direbane mara gani , saboda alumman jihar haryau sabon Gwamnan bai bayyanawa alumman jihar abinda ya tarar daga asusun jihar ba .
Sanan bai bayyana bashin nawa akebin Jihar ko take biba. Haka zalika kwangilar da tsohuwar Gwamnatin ta bata wanda ba a kamala ba , ba’ asan nawa ta kashe kuma nawa zai karasa ayyukan ba.
Kan hakan wakilinmu yaji ta bangaren Gwamnati cikin jawabinsa na cika kwanaki Dari. Gwamna Abdullahi Sule Yace; Gwamnatin sa tayi nasarar daukar Malaman Makaranta a matsayin Ma’aikatan Gwamnatin na dindin din sabanin aikin da abaya sukeyi ta wucin gadi .
Sanan Gwamnatinsa ta kirkire kwamitin duba ayyukan Ma’aikata domin tabbatar da hakokinsu da kuma bada mahimmanci a bakin aiki.
Gwamnan yace; Gwamnatin sa tayi nasarar sanya wutan kan hanya a wasu kananan hukumomi.
Game da aikin filin sauka da tashin jiragen Sama wanda tsohuwar Gwamnatin ta bari. Gwamna Abdullahi Sule yace; titin da aka gina a filin bazai dauki manyan jiragen Sama ba . Saboda haka za su kara kashe makudan kudade domin gabatar da ayyuka masu inganci.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: