Connect with us

LABARAI

Rashawa: An Daure Tsohon Shugaban Kasar El-Savador Shekara Biyu

Published

on

An daure tsohon shugaban kasar El Salvador, Antonio Saca shekara biyu a gidan yari bisa zargin bayar da cin hanci, kamar yadda ofishin babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ya tabbatar.

Tsohon shugaban kasar, mai shekara 54 a duniya, an same shi da laifin yunkurin bayar da cin hanci ga wani ma’aikacin kotu har dala dubu 10 a wani kokarin samun wadansu bayanai da suka shafe shi a kotun, kamar yadda Jaridar La Prensa Grafica ta labarto.

Saca, wanda ya shugabanci kasar daga shekarar 2004 zuwa 2009 ya amince da zargin da ake masa.

Dama tuni tsohon shugaban kasar aka daure shi shekara 10 a gidan yari bisa samun hannunshi wajen almundahana da dala miliyan 300 na al’ummar kasar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: