Connect with us

KASASHEN WAJE

An Kai Harin Makami Mai Linzami Ofishin Jakadanci Amurka Dake Baghdad

Published

on

Wani labari da dumi – duminsa da Legit.ng ta samu daga shafin ‘Spectator Inded’ dake shafin Tuwita ya bayyana cewa an sake kai harin makamin roka mai linzami a kan ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad, babban birnin kasar Iraki.

A cikin takaitaccen sakon da ‘Spectator Inded’ ta wallafa, an bayyana cewa harin ya lalata wani bangare na ofishin jakadanci da ake cin abinci.

“Da duminsa: An kai harin makamin roka mai linzami a ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad a yau, an lalata bangaren cin abinci,” a cewar ‘Spectator Inded’.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko kasa data dauki alhakin kai harin, kazalika, babu rahoton asarar rai.

Ko a ranar 12 ga watan Janairu saida aka kai wasu munanan harin rokoki sansanin sojin Balad da sojojin kasar Amurka ke zaune a birnin Baghdad na kasar Iraki, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

A wancan lokacin, AFP ta ruwaito cewa sojojin Amurka sun arce daga sansanin yayin da sojojin kasar Iraki hudu suka jikkata a harin.Wani jami’in dan sanda a yankin, Salah-Al-Din, ya bayana cewa rokokin sun dira cikin sansanin sojojin saman.

A farkon watan Janairu ne kasar Iran ta harba rokoki masu linzami guda zuwa 20 sansanin sojojin Amurka dake Iraki domin mayar da martani a kan kisan babban hafsan rundunar sojojin Iran, Kassem Soleimani, da Amurka ta yi.

An harba rokokin ne zuwa sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad da misalin karfe 5:30 na yamma, kuma da alamun a kalla sojojin Amurka 80 sun hallaka, a cewar wasu rahotanni.

Amma Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu dan Amurkan ko daya da ya samu rauni a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraki.

Trump ya yi kira ga kasashen Turai, Rasha, Sin, Jamus da Ingila a kan su fita daga yarjejeniyar nukiliya da suka shiga a shekarar 2015.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: