Connect with us

MAKALAR YAU

Wurin Bauta Na ‘Temple of Heaven’ Mai Dadadden Tarihi A Sin (II)

Published

on

Masu karatu, idan ba ku manta ba a makon da ya gabata, kafin na diga aya na koro mu ku bayanai a kan yadda gidan Rediyon CRI Hausa ya ke bayyana tsarin wurin bauta na Temple Of Heaven inda ya ce an gina dakin azumi a kudu da kofar Xitian, wurin da sarakuna su ke yin azumi kafin su yi addu’a. A yamma da dakin ibadan, an kafa hukumar kide-kide domin kula da aikin atisayen kide-kiden yin addu’a. Muhimman gine-ginen da ke cikin dakin ibadan sun hada da dakin Qinian, da na Huangqian, da dandalin Yuanqiu, da dakin adana ‘yan fallen tunawa da kaka da kakannin sarakuna, da dakin azumi da dakin da aka gina da duwatsu kawai, ban da wannan kuma, akwai sauran wurare masu ni’ima kamar su bango mai amsa amo, da duwatsu uku masu amsa sautin amo, da duwatsu bakwai masu alamta taurari bakwai da sauransu. A wannan makon kuma za mu nausa kan sauran muhimman wurare da ke wurin bautar. Inda rahoton gidan rediyon ya ci gaba da cewa:

Muhimman wuraren dake wannan daki, sun hada da dakin Qinian da ke arewacin dakin ibadan aljanna, a baya ana kiran sa da suna dakin Daqi ko dakin Daxiang, an gina shi ne a shekarar 1420 zamanin daular Ming, gine mafi dogon tarihi a dakin ibadan aljannar duniya.

Ko wace shekara, sarakuna su kan gudanar da bukukuwan yin addu’a ga sama a dakin Qinian domin fatan samun yanayi mai kyau da girben hatsi mai albarka, dakin Qinian kewayen daki ne mai launin shudi, saboda launin sama shi ma shudi ne, shi ya sa aka kawata dakin da launin shudi domin alamta sama.

Yayin da masu ziyarar bude ido suka shiga dakin Qinian, idan suka hangi kudu sosai, to, za su ga wata doguwar hanyar da ta yi kudu, har ta zama karama kamar ta fado daga sama. Kan wannan, wani masanin gine-ginen kasar Faransa wanda ya taba kai ziyara dakin ibada na aljanna ya ce, ko da yake gini na zamani ya fi dakin Qinian tsayi, amma bai fi shi girma ba, kuma bai sa jama’a yin zurfin tunani ba kamar yadda suka yi a kan dakin Qinian.

Dakin adana ‘yan fallen tunawa da kaka da kakannin sarakuna yana arewacin dandalin Yuanqiu, kofarsa tana arewa, kuma an kewaye shi da Katanga ko gini, kana daga kudancinsa, an gina kofofin gilashi guda uku, akwai kananan dakuna da dama a ciki, a wannan dakin ne aka adana ‘yan fallen kadarko na gumaka da kaka da kakannin sarakuna. An gina shi ne a shekarar 1530 a zamanin daular Ming, a baya ana kiran sa da suna dakin Taishen, an canja sunan zuwa Huangqiongyu a shekarar 1538. Ya zuwa shekarar 1752 zamanin daular Qing, sarkin Qianlong ya sake gyara dakin, kuma an kawata kofar dakin zuwa launin shudi mai alamar sama. An yi amfani da manyan sanduna guda sha shida domin dogare ginin, wannan tsarin gine-gine yana da inganci matuka.

Ban da wannan kuma, a kan hanyar duwatsu da ke gaban dakin Huangqiongyu, akwai duwatsu guda uku da ake kiransu da suna duwatsu uku masu amsa amo. Idan aka rufe kofar dakin, kana iya jin sautin tafin da ka yi sau daya, a kan dutse na biyu, kana iya jin sautin sau biyu,a kan dutse na uku kuwa, kana iya ji sau uku.

Fuskar bango mai amsa amo da ke kewayen dakin Huangqiongyu, tana da santsi, shi ya sa, ya ke amsa sauti. Idan mutane biyu suka tsaya a gefuna biyu na bangon mai nisan mita dari daya ko biyu tsakaninsu, idan daya daga cikinsu ya yi magana kusa da bangon, dayan zai iya jin maganarsa, sautin muryar zai kara tsawo da ban sha’awa kamar cudanya ce tsakanin dan Adam da gumaka, shi ya sa ake kiransa da suna “bangon mai amsa amo”.

A baya ana kiran dandalin Yuanqiu da suna dandalin yin addu’a ga sama, ko dandalin yin addu’a, kewayen dandalin duwatsu ne mai alamar hawaye uku, wurin da sarakuna suka yi addu’a ga sama a rana ta farko ta yanayin sanyi, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. An gina shi ne a shekarar 1530 zamanin daular Ming, kuma an gyara shi a shekarar 1749 zamanin daular Qing.

Dandalin ya hada da hawa ta sama da tsakiya da kuma ta kasa, yawan matakalan dutsen dandalin yana da nasaba da lamba tara, wadda ake kiran ta lambar sama. A tsakiyar hawa ta sama, akwai wani kewayen dutsen da ake kira dutsen rana ko dutsen tsakiyar sama, idan ka tsaya a kan sa, ka yi ihu ko ka buga shi, za ka ji ya amsa sosai.

Kafin wannan, mun ambata a baya cewa, ana girmama sama a dakin ibada na aljanna ta hanyar amfani da fasahar gine-gine mai inganci, kuma ana nuna kwarjinin sama ne ta hanyar yin amfani da lamba tara. Ban da wannan kuma, an nuna mafarkin Sinawa ta hanyar amfani da launi wato halittu na jin dadin zaman rayuwa.

Muhimmin launin dakin ibada na aljanna shi ne shudi, wanda shi ne launi na sama, ko da yake ba a iya sarrafa launin kamar yadda ake so, amma yana da kyau kwarai. Sama kan samar da rayuwa ga bil Adam da sauran halittu masu rai. Launin kofar dakin Qinian da na Huangqiongyu da bangwayensu shudi ne. Dakin idaba na aljanna kamar duniya ce mai launin shudi. Sararin sama mai launin shudi a bayan dakin idaba mai launin shudi hoto ne da ke alamta mafarki dake cikin zuciyar Sinawa wato bil Adam na jin dadin zaman rayuwa tare a muhallin halittu mai inganci.

Wannan wuri mai dogon tarihi, yana daya daga cikin muhimman wurare da masu yawon bude ido ke ziyara, a duk lokacin da suka zo birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Don haka, duk wanda Allah ya sa ya kawo ziyara kasar Sin, ya yi kokarin zuwa dakin Ibadar aljannar duniya, dake Beijing don kashe kwarkwatan ido. Don haka, kar ku sake a ba ku labara, Malam Bahaushe na cewa, tafiya mabudin ilimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: