Connect with us

LABARAI

Sarkin Fika Ta Shirya Gangamin Fadakar Wa Kan Cutar Zazzabin Lassa

Published

on

Mai Martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Yobe, Alhaji (Dr) Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ya shirya taron gangami tare da wayar da kan jama’ar masarautar sa- ta hanyar tattaro ilahirin masu fada a ji a cikin al’umma, don tatrauna abubuwan da ke haifar da cutar masassarar Lassa domin da daukar matakin kariya, domin a gudu tare a tsira tare.

Da yake qaddamar da jawabi a taron, Mai Martaba Sarkin Fika, wanda Galadiman Fika, Air Commodore Ibrahim Alkali (mai ritaya) ya wakilta, ya bayyana cewa zazzabin Lassa hattsabibiyar cuta ce wadda ke halaka jama’a farat daya.

Bugu da kari kuma, basaraken ya bukaci mahalarta taron da cewa su isar wa sauran al’ummar masarautar saqon da taron ya tattauna kan sha’anin wannan cuta tare da gaggauta bayar da rahoton duk wani motsi mai alaka da cutar zuwa ga cibiyar kiwon lafiya mafi kusa dasu.

“A matsayin ku na shugabanin addini a cikin al’umma, ku ci gaba da gudanar da fadakarwa tare da wayar da kan al’umma a masallatai da coci-coci, ku shaida wa jama’a su kula da tsabtace muhallan su, kuma su kasance masu kula da tsabata a cikin kowane yanayi”. In ji shi.

A nashi haujin kuma, babban jami’in kula da kiwon lafiya a matakin farki (Primary Health Care Coordinator) a qaramar hukumar Potiskum, a jihar Yobe, Abdulrahman Musa ya yaba dangane da yunqurin Sarkin Fika, wanda ya kira da muhimman matakan da za su taimaka wajen riga-kafin kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

A hannu guda kuma, su ma wakilan kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHI), a karamar hukumar Potiskum, Usman Sunusi Bakabe, da takwaransa a karamar hukumar Fika, Mustapha Hassan, ba a bar su a baya ba wajen gabatar da bayanai tare da illolin cutar zazzabin Lassa ga dan Adam.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: