Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Masu Dauke Da Cutar Numfashi Sun Fara Samun Jinya A Sabon Asibitin Huoshenshan

Published

on

Rahotanni daga birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin, na cewa an mayar da rukunin farko na masu dauke da cutar numfashin nan ta coronavirus, zuwa sabon asibitin da aka gini musamman domin yaki da cutar.

Masu fama da cutar sun fara samun kulawar jami’an lafiya, a sabon asibitin na Huoshenshan wanda aka kammala aikin sa cikin kwanaki 10. Asibitin daya ne daga asibitoci 2 da aka tsara ginawa musamman domin yaki da wannan cuta.

A daya bangaren kuma, cibiyar yaki da yaduwar cutar ta birnin Wuhan, ta ce an tsara mayar da wasu karin wurare 3, ciki hadda wani zauren motsa jiki, da wani filin baje koli, zuwa asibitocin wucin gadi na jinyar masu dauke da wannan cuta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: