Connect with us

WASANNI

Courtois Ya Lashe Kyautar Zakaran ’Yan Wasan Laliga Na Janairun 2020

Published

on

An bayyana mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Thibaut Courtois a matsayin gwarzon dan wasan La Liga na watan Janairu bayan kammala wasannin watan Janairun sabuwar shekarar data kama.

Mai tsaron ragar tawagar kasar Belgium din, shi ne dan wasan Real Madrid na farko da ya lashe kyautar a kakar bana saboda kwallo daya ce ta shiga ragar Courtois a watan Janairun daya gabata ya yin da Real Madrid ta ci dukkan wasan La Liga da ta buga da Getafe da Sebilla da kuma Balladolid a watan.

Kawo yanzu ya buga wasannin La liga 20 daga cikin 23 da kungiyar ta fafata, ya kuma hana kwallo ya shiga ragarsa sau 40, kuma wasa 11 kwallo bai shiga ragar Real Madrid ba a gasar ta bana.

Haka kuma Courtois shi ne mai tsaron raga na farko da ya ci kyautar, tun bayan Keylor Nabas a lokacin da yake Lebante kafin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta daukeshi bayan kammala gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014.

Dan wasan Real Madrid na karshe da ya zama gwarzon La Liga na wata-wata shi ne Cristiano Ronaldo a watan Mayun shekara ta 2017 kuma tun bayan tafiyarsa babu wani dan wasa daya sake lashe kyautar.

A ranar Lahadi za a bai wa Courtois kyautar gwarzon dan wasan La Liga na watan Janairu a fafatawar da Real Madrid za ta kara da Celta Bigo a gasar La Liga karawar mako na 24 a filin wasa na Santiago.

Wadanda suka lashe kyautar a bana sun hada da Odegaard a watan Satumba da Karl Toko Ekambi a watan Oktoba da Lionel Messi a watan Nuwamba da kuma Luis Suarez a watan Disamba.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: