Connect with us

RAHOTANNI

Madarasatul Tajjadidul Isilam Ta Yaye Dalibai 42 Karo Na Biyu A Tsiga

Published

on

Makaranta Madarasatul Tajjadidul Isilam da ke garin Tsiga ta karamar hukumar Bakorin jihar Katsina ta yaye dalibai 42 a ranar Asabar din da ta gabata.

Taron yaye daliban wanda ya gudana a harabar makarantar dake garin tsiga kuma taron yaye daliban yasamu halartar wadansu manya manyan malamai da suka fito daga cikin jihar katsina da sauran alummar musulmin jihar bakidaya. Manyan malamai a wajan taron yaye daliban sun hada shugaban kwamitin daawa na jihar katsina Al-Shek Malam Salisu Abdullahi Tata bakori da sauran malamai na chikin garin katsina kar kara bakidaya. Uban taro tsohon janar Mahrazu Tsiga.

Tunda farko dai bayan da aka bude taro da addua ataron walimar yaye daliban saida aka ummurci daliban dasu karanto wadasu ayoyi daga cikin Alkuraani mai tsarki bayan sun kammala karatun ne aka ummurci shugaban kwamitin daawa na jihar Katsina Al-shek Malam salisu tata bakori da sauran wadansu malamai a yayin da suka mike suka fadakar da jamaa akan mahim manci karatun Alkurani mai tsarki tareda nuna faidar yin karatun bakidaya bayan sun kammala ne tsohon burgediya janar mahrazu tsiga ya tofa albarkacin bakinsa agameda taron yaye daliban a yayin da yacigaba da karama iyayen yara kwarin guiwa a wajan cigaba da sanya yayansu a makarantun karatun alkuraani mai tsarki bakidaya, san nan kuma ya ummurci alummar karamar hukumar bakori da jihar katsina da kasa bakidaya dasu cigaba da zaman lafiya da junansu a yanku nan da suke zaune domin suma sucigaba da bada tasu gudummawar na kawo zaman lafiya a bakori da katsina da kasa bakidaya sannan ya shawarici matasan yankin dana kasa bakidaya dasu kaucema yin shaye shaye tareda gudanar da bangar siyasa domin su zama abin koyi ga yara masu tasowa na bayansu bakidaya shima da yake yin nasa tsokacin a wajan taro. Yaye daliban daraktan makarantar ta madarasatul tajjadidul islam malam Abubakar Mohammed Tsiga inda yafara nuna farin cikinsa ga allah da yabada izinin ganin wannan rana da kuma gudanar da taron yaye daliban makarantar. Na wannan shekara karo na biyu sannan ya isar da sakon godiyar sa ga malamai da sauran alumma dasuka zo tayasu murnar gudanar da wan nan alamari a cewar sa suna godiya da fatan kowa ya koma gidansa lami lafiya. Sauran jawabai da suka fito daga baku nan malamai da sauran alummar da sukayi tsokaci a wajan taron yaye daliban yakarkata ne a wajen iyayen yara na cigaba da sanya yayansu makarantun isilamiya tare da sanya ido a kan karatun nasu bakidaya bayan kammala jawaban taron yaye daliban ne wadansu alumma mazauna unguwar sabon gidan madugu dake yankin na tsiga a karamar hukumar Bakorin jihar Katsina Sani Aliyu Mai maganin gargajiya da musa aminu Isiyaka Ibrahim da abubakar suka isar da sakon korafe korafensu na neman gwamnatin jihar katsina ta gyara masu hanyarsu data taso daga cikin garin bakori zuwa tsiga domin dumbin manoma tareda suran alumma su samu hanyar zuwa kasuwa da zuwa asibiti idan hakan ta taso injisu dafatan. Gwamnatin jihar Katsina zata share masu hawaye a gameda wanan alamari
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: