Connect with us

RA'AYI

Yabon Gwani Ya Zama Dole

Published

on

A yanzu haka Jama’a sun daina kiwon dabba sun koma kiwon mutum.

Bisa haka ne wakilinmu ya dira karamar hukumar Danja cikin jihar Katsina, don jin ra’ayin mutane a kan maganar wakilci a siyasa  musamman da ya ke  jihar Katsina jiha ce ta shugaban kasa kuma jaha ce ta jajirtattun mutane da a ke masu kirari da cewa na Dikko Dakin Kara.

Garin Danja helkwatar karamar hukama ce don haka sai wakilin namu ya fara  jin ta bakin wasu kafin wucewarshi Garin Dabai da ke da dinbin tarihi a siyasa.

Alhaji Malam na daya daga cikin yan’siyasar karamar hukumar danja Kuma Dan kasuwa Kuma dattijo a matakin hankali.

Da ya ke amsa tambaya da farko ya yi godiya da ziyarar wakilinmu namu tare da gamsuwa da Abin da ya kawo shi.

Bayan haka ya ce, shi fa babu abin da zance illa ya fara godewa Allah da ya ba su dan majalisar jiha mai amana da sanin ya kamata a harkar siyasa wato Hon. Shamsuddini Abubakar Dabai, wanda shi ne ke wakiltar Danja da Dabai a yanzu haka.

Ya ce, a halin yanzu dai ba a sami kamarsa ba a lokutan baya ma ba a yi kamarsa ba a fadin jihar Katsina a bangarori da daban-daban.

Alhaji Malam ya ce daga cikin abin da ya yi zara a halin yanzu shi ne cika alkawari. Sai girmama na gaba da shi a duk Inda ya sami kansa a gida da waje. Ya kan bai wa yara da manya hakkinsu bangaren sauraren kokensu dare da rana.

Kuma ga shi mai sauraren shawarar jama’arsa dare da rike kowa da muhimmanci a siyasa tun daga karamar hukumar har zuwa ga jaha.

A karshen bayaninsa ne yayi kira ga sauran Yan siyasa da suyi koyi da halin Honorabul Shamsuddini don kawo ci gaban siyasa a siyasance Kuma ya yi fatan Allah ya kara ma sa daukaka da duk sauran ’tan majalisu na jiha da tarayya bakidaya ya ce, amma Honorabul Shamsuddini ya yi ma na dai dai.

Bayan jin ta bakin Alhaji Malam a garin Danja ne sai wakilin namu ya garzaya garin Dabai don jin ko akwai wata damuwa da take damunsu game da wakilcin da suke dashi a jiha zuwa tarayya?

Shigar wakilin namu ba wani daukar lokaci sai ya yi kacibis da wani dattijon basarake mai  suna Mai anguwar Yaro, dake a nan Garin na Dabai  wanda anan take wakilin namu ya sabunta tambayar da ya zo da ita  na jin ra’ayinsu game da maganar wakilci a bangaren siyasa.

Nan take sai dattijo ya kada baki ya ce, ai duk Katsina ba jama’ar da su ka more  Dan majalisar kamar garin Danja da Dabai.

Mai Anguwa Yaro ya ce a halin yanzu su  Honorabul Shamsuddini Citoma Dabai Babu, inda bai tabawa da kowa ya ke farinciki da hakan kuma she ke fitar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari kunya a wannan yankin.

Ya ce, idan za a tabo harkar lafiya ne to kwanaki ya bayar da makudan kudi, don sayen maganin da za a bai wa jama’a.

Maganar tsaro kuwa akwai tsari na musamman da ya ke da shi na taimaka wa masu tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a

Mai Anguwa me ya kara da cewa magana a kan harkar ilmi kuwa matasa da yawa sun sami tallafin a matakai da dama daga jami’a zuwa kasa.

Sama wa matasa aikin yi kuwa dole mu yi ma sa jinjina ta musamman kuma ga taimako da ya ke bayarwa a duk Inda a ke bukata, kamar aure, suna, rashin lafiya da Islamiyoyi.

Kuma ya tabbatar da cewa shi Honorabul Shamsuddini Ciroman Dabai a Koda yaushe ya na tare da jama’arsa kuma yana sauraren kokensu kuma ya na shigar da kokensu a majalisar tarayya don kawo ci gaba da sauke nauyin da Allah ya dora ma shi.

Don haka ne mu a gurinmu Hon. Shamsuddini ya yi ma na daidai.

Binciken da wakilin namu ya gudanar game da shi wannan Dan majalisar mai wakiltar Danja da garin Dabai mai word akalla 10 ya nuna cewa tabbasa dan majalisar ya na tare da jama’arsa a kowani lokaci.

Kuma bugu da kari bisa aikin da ya ke yi na alkairi ya sa kowa na nuna kauna gare shi da fatan alhairi gare shi.

Kuma bincike ya nuna cewa shi ba ya kyamar kowa duk lokacin da ya ke gida, to jama’a ne ke yin dafifi a gidansa don samun abin rufin asiri.

Hakan ya sa babu wata jambiyar  ko wani mutum da ke da tasiri a siyasance face Hon. Shamsuddini Abubakar Ciroman Dabai a wannan yankin.

Hakan ya sa na yi wa wani matashi dan jam’iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa tambayar ko me zai ce game da harkar wakilci a karamar hukumar Danja?

Sai matashi ya kada baki ya ce a gaskiya duk adawar mutum sai ya yabi Hon. Shamsuddini Ciroman Dabai saboda halaiyarsa na kirki don shi kowa nashine ga kakuri da sanin ya kamata ga shi ba ya daukar zuga ko gulma, wanda haka a ke son shugaba ya zama don haka gaskiya Honorabul Shamsuddini Abubakar yayi mana daidai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: