Connect with us

NOMA

Har Yanzu Dokar Hana Shigo Da Taki Nijeriya Na Nan Daram – CBN

Published

on

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya jaddada cewa, dokar da ta dakatar da shigo da takin zamani samfarin NPK ta na nan daram. A saboda hakan ne CBN ya kuma bayar da umarnin cewa, babu wani dillali da a ka bai wa damar ya bayar da fom na ‘M’ na shigo da dukkan wani nau’in takin zamani samfarin NPK.

Fom din na ‘M’ wani kundi ne wanda dukkan mai shigo da dukkan wasu kaya zuwa cikin kasar nan sai ya cika shi tukunna kafin ya samu izini.

A cikin wata sanarwa da a ka turawa dukkan dilolin da kuma sauran alummar gari, Darakta na sashen musaya da kasuwanci na babban bankin Nijeriya CBN ta na dauke ne da sa hannun A.S. Jibrin, inda kuma sanarwar ta kara da cewa, duk wanda ya karya dokar, zai fuskanci takunkumi.

A cewar babban bankin Nijeriya CBN, a saboda hakan, dukkan wani dillalin da ya samar da fam din na ‘M’ don shigo da dukkan wani samfarin takin na NPK zuwa cikin kasar nan, da kuma sauaran kaya, za’a kakaba masa takunkumi har ma’aikatan su da suka gudanar da hada-hadar yin hakan.

Babban bankin na Nijeriya ya jadda da cewa, a saboda hakan, ya zama wajibi akan dukkan masu shigo da kayan, dasu tabbatar da sun cike fam din na ‘M’ tare kuma da yin rijistar da fam din na ‘M’ ga dukkan dilan da aka amince dashi a dukkan lokacin da zasu shigo da kayan cikin kasar nan.

Babban bankin na Nijeriya CBN shine ya kirkiro da wannan tsarin na yin hada-hadar ta hanyar yin amfani da na’urar zamanida bankin na CBN ya samar tare da hadin gwaiwa da hukumar hana fasakauri ta kasa.

Fam din ‘M’, wata ka’ida ce wacce dole ne sai dukkan wani mai shiho da kaya daga kasar waje zuwa cikin kasar nan dole sai cike shi tukunna kagin a yarje masa ya shigo dasu.

Wa’adin fam din na M, ya na kaiwa kwanaki 180 kafin ya daina yin aiki, inda kuma ga daukacin masu shigo da kaya cikin kasar nan, suke da tsawon kwanuka and 365, bayan haka kuma ana iya kara wa’adin kwanuka 180, inda kuma ga sauran masu shigo da kaya zuwa cikin kassr nan, ake kara masu tsawon kwanuka 365.

Har ila yau, duk wata kara dagawa za’a sake yi, dole sai idam babban bankin Nijeeiya (CBN) a amince da hakan tukunna, inda hakan ya nuna wajibi ne ga dukkan wani dila dake son shigowa da kaya cikin kasar nan daga kasar waje, sai ya cike fam din na ‘M’ tukunna.

Bugubda kari, babban bankin na Nijeriya yana gudanar da hakan ne ta hanyar yin aiki kafada da kafada da hukumar hana fasakauri ta kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: