Connect with us

JAKAR MAGORI

Kotu Ta Garkame Mutum Uku A Gidan Yari Bisa Shiga Kungiyar Asiri

Published

on

A ranar Litinin ce, kotun Ikeja ta garkame wasu mutum uku a gidan yari, bisa tuhumarsu da fadawa cikin kungiyar asiri da kuma mallakar makamai ba tare da ka’ida ba. Su dai wadanda ake tuhumar sun hada da Emmanuel Godwin dan shekara 28 da Onyeka Sunday dan shekara 26 da kuma Jamiu Abiola mai shekaru 37, dukkanin su suna zaune ne a yankin Alapere da ke cikin Jihar Legas, inda suke fuskantar hukumar hada kai domin aikata laifi.

Sai dai sun musanta laifin da ake tuhumar su da shi.

Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, ASP Raji Akeem, ya bayyana wa kotu cewa, wadanda ake zargin sun aikata wannan laifin ne tun a ranar 10 ga watan Junairu a yankin Mile 12 da ke cikin Jihar Legas. Akeem ya kara da cewa, ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan da suka sami bayanai sirri. A cewarsa, wadanda ake zargin ‘ya’yan kungiyar asiri ne da ake kira da suna AYE da kuma EIYE.

“’Yan kungiyar asirin guda biyu su na fada da junansu lokacin da ‘yan sanda suka isa wajen, sai su ka samu nasarar damke mutum uku, yayin da sauran su ka gudu,” in ji shi.

Akeem ya ci gaba da cewa, an kama su ne da bindigogi kamar haka, babbar bindiga mai sarrafa kanta da kananan bindigojin kirar gida guda biyu da kuma karamar bindiga mai sarrafa kanta. Ya ce, wannan laifi ne da ya saba wa sashe na 42 da 330 da kuma 411 na dokar manyen laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, sashe na 411 na dokar manyen laifuka ta tanadi daurin shekara biyu a gidan yari ga duk wanda a ka samu ya aikata irin wannan laifi.

Alkali mai shari’a Misis O. A Layinka, ta bayar da belin wadanda ake tuhuma a kan hudi na naira 500,000 ga kowannensu tare da mutum biyu masu tsaya musu. Layinka ta dage sauraron wannan kara har sai ranar 25 ga Fabrairu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: