Connect with us

JAKAR MAGORI

Uba Ya Azabtar Da Dansa Bisa Satar Kifi

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun ta damke wani mutum mai suna Idowu Sikiru, bisa laifin azabtar da dansa mai suna Segun Sikiru dan shekara biyar. Shi dai wanda ake zargin yana zauna ne a layin Itowo cikin yankin Oke Sopen da ke garin Ijebu Igbo, an dai bayar da rahoton mutumin ya azabtar da dansa, inda ya kone masa takashi saboda ya saci kifi. An dai samu nasarar damke shi ne baya da mutane su kai wa ‘yan sandan yankin Ijebu Igbo suka sami rahoton faruwar lamarin cewa, wanda ake zarginm yana kokarin kashe yaro karami.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa, lokacin da suka sami rahoton faruwar lamarin, nan take suka tura tawagar ‘yan sanda zuwa wajan da lamarin ya afku, sannan suka cafke wanda ake zargi. Ya kara da cewa, mahaifin ya saka faranti a cikin wuta, inda ya manna wa yaron a takashinsa wanda ya yi sanadiyyar kone wa yaron takashi. “Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin ya tuhumi yaron da satar fikin miya, inda ya saka faranti a wuta sai da ya yi jawur, sannan ya manna wa yaron a takashinsa, inda ya raunata yaron a takashinsa. “Haka kuma ya yi amfani da wannan faranti wajen kone yaron a hannunsa da kuma bakinsa. An dai garzaya da yaron zuwa asibiti,” in ji shi.

Oyeyemi ya ci gaba da cewa, kwamishinan ‘yan sandar jihar, Kenneth Ebrimson, ya bayar da umurnin a mika wanda ake zargi gas ashen rundunar ‘yan sanda masu yaki da safarar yara, domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: