Connect with us

LABARAI

Gwamnan Zamfara Ya Yi Barazanar Sauke Marasa Taimakon Al’umma A Mukamansu

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Hon Bello Muhammad Matawallen Maradun ya bayyana cewa, duk wanda ya ba shi mukamin siyasa ko kuma al’umma suka zabe shi ya ki taimakon al’ummarsa lallai zai rasa kujerarsa.

Gwamna Matawallen Maradun ya bayyana haka ne a wajan sanya hannu a kasafin kudin wannan shekarar ta 2020 da Kakakin Majalisar Hon Muazu Magarya ya kawo masa a gidan gwamnati da ke Gusau .

Hon. Matawallen Maradun ya bayyana cewa, “kammala bitar kasafin kudin da ‘yan majalisar Dokokin na jihar suka yi a cikin makonni shida abun yabawa ne kuma wannan zai ba mu damar cigaba da ayyukan more rayuwa ga al’ummar jihar Zamfara”.

Gwamna Matawallen Maradun ya kuma tabbatar da cewa, kowace Ma’aikata za su gudanar da ayyukan ma’aikatar su da kansu , dan haka na ke kira ga ma’aikata da masu mukaman siyasa da su ji tsoran Allah wajan tafiyar da ayyukan su, dan ba za mu lamuncin zagon kasa ba wajan tafiyar da ayyukan al’umma jihar ba.

Da ya koma kan ‘yan majalisun Dokokin jihar, Gwamna Matawallen Maradun ya tabbatar da cewa, kowane dan majalisar akwai aikin da gwamnati za ta gudanar a mazabar sa kuma suna cikin kasafin kudin, dan haka su ne za su jagoranci duba ayyukan dan ganin an yi ayyukan masu inganci ga al’umma .

 

A jawabin Kakakin majalisar Hon Ma’azu Magarya ya bayyana cewa a shekara da ta gabata 2019, Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya gabatar masu da kasafin kudin na shekarar ta 2020 na Naira biliyan 182 , 789,37858, kuma sun yi wa kasafin karatun ta natsu kuma duk wadnda ke da alhakin kare kasafin kudin daga sasan ma’aikatun jihar sun kare, sannan yanzu sun kammala suka gabatar wa Gwamnan inda a take ya rattaba wa kasafin hannu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: