Connect with us

HANTSI

Matsalolin Da Zargi Ke Haifarwa A Tsakanin Ma’aurata

Published

on

Yau za mu yi tsokaci ne a kan illar zargi a tsakanin maaurata. Wannan kalma ta zargi ba kalma ce me dadi ba, sai dai duk da haka mutane a yau sun doru a kai, ba ga mace ba, ba ga namiji ba. Muna cikin wani zamani na rashin yadda ya yi yawa a cikin alumma musamman ga maaurata, wadanda su aka fi so su yadda da junansu fiye da kowa a duniya, sai gashi a yau mace ba ta yarda da mijinta ba, haka kuma miji bai yarda da matarsa ba.

Yana da kyau ta bangaren mace ta zama me yarda da mijinta kar ta zama me yawan zarginsa da wasi-wasi a cikin al’amuran da yake yi. A duk lokacin da aka samu gidan da akwai zargi a cikin zamansu, to wannan gida albarka ba ya shiga ciki sai fitina da tashin hankali a kullum. Haka miji ya daina zargin matarsa ta kowacce fuska, ya tsaya su fahimci juna, domin da a ce ana zama da zargi, to gara a ce an hakura da auren baki daya don zai fi alheri. Haka ko a tsakanin yara ne iyaye su daina zarginsu a kan wani abu, hakan zai fi haifar da nitsuwar zuciya.

A duk lokacin da mace ta matsa wa kanta da zargin miji, karshe za ta hadu da wata larurar saboda kullum lissafi da tunaninta miji na can wani wuri yana aikata ba dai-dai ba. Idan yana gaisawa da wata, tunaninta kila budurwarsa ce ko bazawararsa, yana da kyau mu yi zama da tsarkakken zuciya a duk inda muke.

Haka ma da kowadanne irin mutane zama ya hada ku to ki kyautata zato. Ta kai a yanzu mace kan iya bibiyar duk motsin mijinta saboda tana zarginsa, haka shi ma namiji kan iya bibiyar matarsa saboda bai yarda da ita ba, saboda Allah a nan shin me muke son nuna wa yaran da muka haifa? Ko kawai muna so mu nuna musu zama da amana sun kare a duniya? Yadda muka dauka a yanzu a kan abokan zamanmu da yaranmu da yanuwanmu za su dora fiye da haka, karshe a yi ta samun matsaloli da fitintunu a cikin alumma.

Duk macen da za ta kasance me zargi to kuwa dole za ta zama marar wadatar zuci, don a duk lokacin da miji ya yi mata alheri to fa gani za ta yi ya yi wa wata dubunsa, wannan zai sa ba za ta yaba ba balle ta yi godiya. Mu sani a mafi yawan lokuta muke haddasa wa kanmu matsaloli wanda ba za mu iya shawo kansu ba. Mace ta sani mijinta shi ne mutum na farko da zai zamo amintaccenta sai kuma yarantasu su biyo baya, haka shi miji wadannan su ya kamata ya yarda da su ya kuma amince da su saboda sune makusantansa fiye da kowa. Aure da yawa sun mutu, wasu sun samu tangarda an warware, wasu har yanzu ana fuskantar matsala don ba a gano bakin zaren ba duk a dalilin zargi. Mata mu gyara dabiunmu a kan mazajenmu musamman a bangaren abin da ya shafi zargi, duk wata mace rufin asirinta shi ne mijinta, gatanta kuma ya kasance cikin daraja a cikin alumma, saboda haka mu rage zargi a kan mazajenmu, mu kyautata musu zato me kyau a cikin rayuwarsu, hakan zai sa mace ta kasance abin kwatance a cikin alumma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: