Connect with us

LABARAI

Za A Yi Amfani Da Rahoton Taron kasa Na 2014 Wajen Gyaran Tsarin Mulki

Published

on

A ranar Laraba, Kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran Tsarin mulki ya shaida cewar zai duba rahoton taron kasa na 2014 wajen tafiyar da aikin da ke gabansa.

Haka zalika kwamitin ya kuma yi alkawarin amfani da kwamitin da Gwamna Nasir el-Rufai ke jagoranta na sake sake fasali.

Shugaban Kwamitin kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Obie Omo-Agege shi ne ya yi wannan alkawarin a lokacin da shugaban majalisar Dattabai Ahmed Lawan ya kaddamar da kwamitin a Abuja.

Shugaban Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da taron kasa na 2014 ne a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2014 inda wakilai 492 suka hadu suka tattauna a kan yadda za a sake wa kasar nan tsarin gudanarwa.

 

Manyan kusoshi a yayin taron kasar sun hada da shugabanta Alkali Idris Kutigi (mai ritaya), mukaddashin shugaba Farfesa Bolaji Akinyemi da kuma Dakta balerie Azinge, a matsayin sakatarensu.

 

Shugaban kwamitin bin tsarin mulkin, Omo-Agege ya ce; “a yayin aiwatar da wannan aikin na kasa, wannan kwamitin ba shakka zai duba canji na tsari na shida domin samar da sabbin abubuwa kamar kafa majalisun kasa da na jihohi, Kotun batutuwa kafin zabe, kotunan batutuwan da suka shafi gabanin zaben gwamna da na shugaban kasa, tare da kayyade wa’adin tattara dukkanin abubuwa kafin gudanar da babban zabe.

 

“Sannan, za mu yi la’akari da bukatar juyin iko, cikakken tsarin bai wa kananan hukumomi cin kashin kai, cikakken ikon cin kashin kai ga bangaren shari’a a sashin zartas da hukunci, shigar da matasa a dama da su wurin gudanar da mulki, duba yadda za a gyara banbanci a tsakanin jinsin mata da maza,” A cewar shi.

 

Ya kara da cewa kwamitin zai kuma yi la’akari wajen shigar da masu ruwa da tsaki da kungiyoyi daban-daban da suke fadin kasar nan wajen aiwatar da aikin da ke gabanshi.

 

“Baya ga wannan, wannan kwamitin zai kuma yi amfani da shawarwarin babban taron kasa na shekarar 2014 da kwamitin da gwamna Nasir el-Rufai ya shugabanta kan sake fasali,” A cewar shugaban kwamitin na majalisar dattawan.

 

Shi kuma a jawabinsa, shugaban majalisar dattawan kasar nan Ahmad Lawan ya shaida cewar, “Muna tsammanin wannan kwamitin zai tuntubi kungiyoyin jama’a da kungiyoyin fararen hula. Wadanda sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta INEC, masu ilimi, kafafen yada labarai, da wadanda lamarin ya shafa.

 

“Wannan aikin na bukatar wadataccen lokaci, kudade da kwararrun masana. Saboda gyaran kundin tsarin mulki ba aikin rana daya ba ne,” A cewar shi.

 

Kodayake da fari shugaban majalisar ya gabatar da sunayen mutum 56 a kwamitin, amma daga bisani ya kara Ifeanyi Ubah (Anambra ta kudu)  da Betty Apiafi.

 

Jerin shugabanni da mambobin kwamitin mai mutum 58 sun hada da; Shugaban masu rinjaye na majalisar Yahaya Abdullahi, da mataimakinsa Robert Ajayi Boroffice, da mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawan Aliyu Sabi Abdullahi, shugaban marasa rinjaye Eyinnaya Abaribe, mataimakin shugaban marasa rinjaye Emmanuel Bwacha, Mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye Philip Aduda da kuma Mataimakinsa Sahabi Ya’u.

 

LEADERSHIP A Yau Juma’a, ta nakalto cewar kowace jiha tana da wakili guda daya cikin wannan kwamitin da suka hada da: Theordore Orji (Abia), Aishatu Ahmed Dahiru (Adamawa), Stella Oduah (Anambra), Albert Bassey (Akwa Ibom), Haliru Jika (Bauchi), Diegi Biobakara (Bayelsa) da kuma Gabriel Suswam (Benue).

 

Sauran sune: Abubakar Kyari (Borno), Gershom Bassey (Kuros Riba), James Manager (Delta), Sam Egwu (Ebonyi), Matthew Urhoghide (Edo), Bamidele Opeyemi (Ekiti), Ike Ekweremadu (Enugu), Danjuma Goje (Gombe), Rochas Okorocha (Imo), Sabo Mohammed (Jigawa), Uba Sani (Kaduna), Kabiru Gaya (Kano), Baba Kaita (Katsina), Adamu Aliero (Kebbi), Smart Adeyemi (Kogi) da kuma Sadik Umar (Kwara).

 

Sanatocin da suka hada da Oluremi Tinubu (Legas), Abdullahi Adamu (Nasarawa), Mohammed Sani Musa (Niger), Ibikunle Amosun (Ogun), Nicholas Tofowomo (Ondo), Bashiru Ajibola (Osun), Teslim Folarin (Oyo), Hezekiah Dimka (Plateau), George Sekibo (Ribers), Aliyu Wammako (Sokoto), Yusuf Yusuf (Taraba), Ibrahim Gaidam (Yobe) gami kuma da Hassan Gusau (Zamfara) dukkaninsu suna cikin kwamitin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: