Connect with us

LABARAI

Ba Mu Ke Yi Wa Jama’a Fashi A Dambam Ba, Cewar ‘Yan Sandan Bauchi

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Phillip S. Maku ya karyata wani bidiyon da ke yaduwa a kafafen sadarwar zamani da ke nuna yadda ‘yan sanda ne ke yi wa al’umma fashi da makami a daidai karamar hukumar Danbam da ke jihar Bauchi.

A wani taron manema labaru da ya kira na gaggawa a yau din nan, Kwamishinan ya shaida cewar yada bidiyon ba wai kawai zallar karyace ba ma, a’a bata musu suna ne da musguna musu wanda ya shaida cewar hakan bai dace ba, ya kuma ce; kana ba zai taimaka wa Rundunar wurin yaki da ‘yan ta’adda ba.

LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar wasu da ba kai ga tantance ko su waye ba, sun sake wani faifayin bidiyo mai nisan minti daya da sakon ashirin da biyu da ke nuna cewar ‘yan sandan caji ofis din Dambam ne ke yawan yi wa jama’a fashi da makami, lamarin da ya kai su ga fusata da fatattakar ‘yan sandan.

A fashin da aka yi a daren jiya Talata mutanen sun zargi ‘yan sanda da shiga cikin jama’a hadi da yi musu fashi da makamai, kana sun nuna cewar bayan da suka fattaki ‘yan sandan, jami’an ‘yan sandan sun arce sun bar motarsu da wayar salula ta wani dan sanda.

A bidiyon an kuma yadda aka jitta wasu mata ciki har da yara kanana.

Sai dai a taron manema labarun da kwamishinan ‘yan sandan CP Phillip S. Maku ya kira, ya bayyana cewar ‘yan sandan sun gudu sun bar motarsu ne a sakamakon kokarin da mutanen suka yi na jikkata su, “Bayan da ‘yan fashin suka yi wa jama’a fashi, jami’anmu na ‘yan sanda sun je domin taimaka wa jama’a, nan fusatattun direbobi suka zargi ‘yan sanda da cewar sune suka musu fashi, hakan ya janyo dole ‘yan sandan su kauce domin daidaita lamura, a kokarinsu na barin wajen sai jama’a suka bisu,”

Kwamishinan ya tabbatar da cewar motar da ake yadawa tabbas ta ‘yan sanda ce, amma dai sun je wurin ne taimakon jama’a, sai kuma jama’an suka farmakesu da zargin cewar sune suke yin fashi wa jama’a, lamarin da ya tilasta wa ‘yan sandan arcewa su bar motar tasu a wajen.

Hanyar Dambam dai ya hada kan titin da ya fito daga Kano zuwa Maiduguri da kuma Bauchi zuwa karamar Dambam.

‘Yan sanda sun gabatar wa ‘yan jarida wakilin Hakimim Dambam, Lamido Musa Sulaimai da wani direban da lamarin ya faru a kan idonsa Umar Muhammad daga jihar Kano, sun kuma yi bayani kan yadda abin ya faru; don haka za mu kawo cikakken rahoton a fitowar jaridarmu ta gobe.

Cikakken labarin na biye:
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: