Connect with us

RAHOTANNI

Kansilan Mazabar Sharada Ya Biya Wa Matasa 300 Kudin Jarabawar JAMB

Published

on

Kakakin majalisar kansiloli na karamar hukumar Birnin Kano.Hon.Yusuf Baba Wapa ya tallafa wa matasa 300 da foma-famai na jarrabawar “JAMB”a yakin mazabarsa.

Da yake jawabi a wajen taron daya daga cikin jagororin siyasar APC a karamar hukumar Birni, Manajan darakta na hukumar “KAROTA” Baffa Babba Dan’agundi ya yabawa irin kokarin aikin kwarai na Kansilan mai wakiltar mazabar sharada da yakamaci duk wani mai mulkin siyasa ya rika aiwatarwa.

Ya ce, Hon. Yusuf Baba Wapa tun kafin ya zama zababben kansila na sharada yana yin ayyuka na alkhairi duba da cewa tarone na siyasa amma dinbin mutane da suka halarta ya nuna irin halayyarsa ta kulawa da al’umma.

Ya yi kira ga Kansilan akan ya cigaba da dabi’arsa ta mutunci da biyayya. Yana da dama duk takarar da yaso zai iya yi a karamar hukumar Birni in dan abin duniya ne amma ya ce, kansila yake so ya yi.

Baffa ya ce, lokacin da zai tsaya kansila suka ce masa wai mai zaka yi da kansilan nan? Amma daga lokacin da ya zama kansilan da albashinsa da duk wani alawus ya ribanyasu fiye da nunki ya bayar a mazabarsa da sauran mazabu, Ina maka fatan kujera ta gaba kuna duk abinda ka shigo da bukata zamu goyi baya mu mu tayaka nema a wurin Allah ya baka”

Shima a nasa jawabin Kansilan na mazabar Sharada ya ce, daga dalilinsa na tallafar matasan shi ne don bada gudummuwa wajen ciyar da ilimi gaba a karamar hukumar Birni domin da wannan ilimi kowa zai taimaki kansa ya taimakawa ‘yan uwansa da iyayensa  da al’umma da kasa baki daya.

Hon.Yusuf Baba Wapa ya ce, kullum a shirye yake wajen bada irin wannan gudummuwa ta cigaban ilimi da sauran fannono na rayuwa kamar yanda ya saba shekaru da yawa.Da sunso su baiwa Mutane 200 amma saboda mutane da dama na bukata kuma basuda dama su sayi wannan fom sai suka kara wanda mutane da suka  samu yakai 300 kuma yanasa ran da yardar Allah a shekara mai zuwa ya ribanya.

Hon.Yusuf Baba Wapa ya yi kira ga yan siyasa da sauran mutane dake tallafawa cigaban al’umma akan sufi bada muhimmanci wajen tallafawa bunkasa harka ta ilimi da sana’oi da lafiya domin idan mutum yazo ka bashi kudi yau gobe yazo baka bashi ba watakila ma ya zageka amma inka baiwa mutum dama ta samun ilimi ko sana’a ka kafa rayuwarsa da shima zaije ya taimaki mutane da zai amfanar da yawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: