Connect with us

LABARAI

Jihar Kebbi Za Ta Yi Amfani Da Naira Biliyan 650 A Gyaran Wuraren Bikin Kamun Kifi

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamnanta Abubakar Atiku Bagudu ta ware Naira Biliyan 650 saboda yin gyaran wuraren da zaa gudanar da bikin kamun kifi na kasa da kasa a garin Argungu a jihar Kebbi wanda kuma aka shirya za ayi shi a farkon watan Maris na shekarar 2020.

Wannan bayanin ya fito ne daga  kwamishinan ayyukka na jihar, Alhaji Abubakar Chika Ladan, lokacin da ayak ganawa da manema labarai, jim kadan bayan da suka kammala bayan  da suka kammala taron majalisar zartarwa na jihar, wanda aka yi  jiya shekaranjiya Laraba a fadar gwamnatin jihar ta Kebbi da ke Birnin-Kebbi.
Wannan wani cigaba ne ko kuma halin da ake cike akan shirye- shiryen da ake yi  wanda ya shafi bikin kamun kifi na Argungu wanda kuma za ayi a wata mai zuwa wato Maris a jihar ta Kebbi . Ya cigaba da bayyana cewar “ babban  kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa sun kai ziyarar aikin a wuraren da gwamnatin ta bayar da kwangilar gyarawa, domin tabbatar da cewar an gudanar da shi bikin cikin nasara da kuma kayatarwa. Wannan al’amarin ya kasance shi biki ne wanda zaa gaiyato mutane daga kasashen Turai saboda raya aladdun gargaji na al’ummar jihar ta Kebbi ”.

Bugu da kari kuma ya bayyana cewar an kafa kwamitoci daban- daban don tabbatar da an gudanar da shi bikin cikin nasara. Ya cigaba  da bayanin cewar” Idon an  kai ga zaben ita  ranar da zaa gudanar da shi bikin a cikin farkon  makon farko na watan uku, kwamishinan watsa labarai zai bada sanarwa ta musamma, ga duk al’ummar kasa da kuma sauran kasashen duniya ta hanyar gudanar da taron manema labaru na kasa a Abuja”.
Hakanan ma ya kara jadd ” wuraren da zaa gyara sun hada da matan fada, fishing billage, wani sashe na otel din grant fishing ,da kuma wasu tituna da ke zuwa wuraren da zaa gudnar da bukukuwan kamun kifi da kuma sauran wasu wurare a garin na Argungu don tabbatar bikin ya kayatar. Bugu da kari kuma yace” zaa hada tawagar da zata je Abuja don bayyana wa Ministan watsa labaru da aladun gargajiya, da  kuma sauran wasu hukumomi gwamnatin tarayya  masu ruwa da tsaki ga harakokin aladun gargaji da kuma masu zuba jari kan habaka aladun gargajiya ga jahohin kasar nan.
Daga karshe dai yayi kira ne da al’ummar  jihar Kebbi da sauran alummar kasar nan kan bada goyon bayansu da kuma zuba jari ga bikin na kamun kifi da zaa gudanar a farkon watan uku na shekara ta 2020.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: