Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Wace Irin Gudunmawa Sana’ar Jigilar Kayayyaki Ke Yi Wajen Yaki Da Cutar COVID-19?

Published

on

Ba a dakatar da taimakon jinya da jigilar kayayyaki ba, bayan an dauki matakin “Hana shiga da fita” a birnin Wuhan.
Jiragen sama marasa matuka guda 3 suna kaiwa da kamowa har sau 18 don jigilar kayayyakin jinya 27 cikin gaggawa ga asibiti mai kula da annoba na birnin Wuhan, saboda ana jigilar kayayyakin bukatun yau da kullum da kuma na’urorin jinyya cikin lokaci, an gina asibitin Huoshenshan cikin kwanaki 10 kacal, ban da wannan kuma, an yi jigilar naman shanu da na rago da yawansa ya kai ton 400 cikin kwanaki 6 daga jihar Mongoliya ta gida dake arewacin kasar Sin zuwa Wuhan, wadanda suke da nisan kilomita 1500. Sana’ar jigilar kayayyaki mai karfi dake da nagartaccen tsari wadda ake yi ba dare ba rana ta bada tabbaci wajen sufurin kayayyakin yaki da cutar da biyan bukatun jama’a, har ma da kiyaye zaman oda da doka.
Wadannan nasarorin da sana’ar ke da su ya dogara da hazaka da ake da shi da kuma karfin bada hidima dake sahun gaba a duniya. An ce, yawan kayayyakin da sana’ar jigilar kayayyaki ta sarrafa a shekarar 2019 a kasar Sin ya kai fiye da biliyan 60, matakin da ya sa ta kai matsayin farko a duniya cikin shekaru 6 a jere, adadin da ya kai kashi 50 cikin dari na duk duniya gaba daya. Dadin dadawa, kamfanonin jigilar kayayyaki na kara karfinsu a cikin wannan muhimmin lokaci, za su kara hazaka nan gaba.

(Mai Fassarawa: Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: