Connect with us

LABARAI

Hukumar NDLEA Ta Lalata Miyagun Kwayoyi Kilogiram 16,142 A Bauchi

Published

on

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta lalata haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 16,142 a jihar Bauchi.

Kwayoyin da suka kama din sun hada da Tiramudol, Rohypnol, Diazepam, Edol-5, Cannabis Satiba da Cough syrups hadi da Kodin.
Da ya ke jawabi a lokacin lalata kwayoyin da suka yi a kauyen Gida Daya Dungal da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos a makon jiya, shugaban hukumar ta NDLEA na kasa, Kanal Muhammad Abdallah, ya ce an kwace kwayoyi masu yawan ne lura da yawan jama’an jihar.
Ya kuma ce hukumar tasu ta kara azama da himma domin tabbatar da dakile masu ta’anmuli da kwayoyi sai ma yake gargadin masu safaran shi da su tuba su daina, a cewarshi duk wanda suka cafke na sha ko na sarafan shi za su dandana mishi kudarshi.
Abdallah, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Barista Barrister Oluruntunba Femi ya shaida cewar; sun iya gano cewar yawan ta’anmuli da miyagun kwayoyi na kara haifar da ayyukan ta’addanci.
“A tsakanin watan Janairun 2020 zuwa yau, hukumarmu ta lalata kwayoyi masu nauyin kilogiram 150,739.0508. A jihar Legas kwayoyi mai nauyin likogiram 100,035.418 muka lalata. A jihar Ogun kuwa, mun lalata kwayoyi mai nauyin kilogiram 34,560.9438 a makon da ta shude,” A cewar shi.
Ya kuma shaida cewar shan miyagun kwayoyi na kara katsanta a tsakannin matasa da mata wanda ya nuna hakan a matsayin abin takaici.
Ya kuma shaida babbar kalubalen da ke addabar su ita ce matsalar masu safaran kwayoyin sai ya nemi hadin kan jama’a da su mara musu baya wajen tona asirin dukkanin wuraren masu saidawa ko safaran kwayoyi a cikin al’ummominsu domin dakile aniyarsu.
Ya ce, Hukumarsu da ke Bauchi tana samun gagamar hadin kai wanda hakan na kara basu damar shawo kan matsalolin, sai ya jinjina wa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad a bisa hadin kan gwamnatinsa wajen shawo kan matsalolin masu shan miyagun kwayoyi a jihar.
A jawabinsa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya shaida cewar lalata haramtattun kwayoyin ya kamata ya zama abin kaito da takaici ga dillalan da suka nutsa dukiyarsu suka tsayo kana hukumar ta kwace hadi da banka musu wuta.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Baba Tela ya bayar da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da mara baya wa shirin yaki da ta’anmuli da miyagun kwayoyi a jihar, sai ya kalubalanci iyaye kan kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.
Ya yi amfani da damar wajen yaba wa hukumar NDLEA a bisa kyakkyawar hadin kai da ake samu a tsakaninsu da bangaren shari’a dangane da aiyukansu, sai ya nemi jama’a da su shigo a dama da su wajen taimaka wa hukuma ta yi aikin hana shan kwayoyin da suka kasance masu illa ga jama’a.
A jawabinsa na maraba, Kwamandan NDLEA na jihar Bauchi,  Segun Oke, ya shaida cewar hauhawar shaye-shayen miyagun kwayoyi na kara haifar da matsalolin tsaro a cikin al’umma.
Ya nuna cewar matsalolin da suka hada da irin shaye-shaye suna haifar da sara-suka, fashi da makami, garkuwa da mutane, addabar jama’a a jiha da ma kasa baki daya.
Uwa-uba ya ce shan miyagun kwayoyi na haifar da lalata lafiyar dan adam sai yayi gargadin jama’a su daina amfani da kwayoyin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: