Connect with us

LABARAI

Aikin Gwana Nafisa Yana Daukaka Darajar Musulunci Da Musulmi – Dr. Sunusi Bichi

Published

on

Shugaban Makarantar Kwalejin Ilmi tare da share fagen shiga Jami’a ta Kano, Dakta Sunusi Yakubu Bichi, ya bayyana aikin Hafiza Gwana Nafisa Yusuf Bichi na wallafa faifen CD na Karatun Alkur’ani mai girma tare da sauran rubuce-rubuce da kuma hidima da ta ke yi na koyar da Littafin Allah mai girma, maza da mata yara da manya a garin Bichi da Kano, a matsayin wani abu ne da ya ke daukaka darajar Musulunci da kuma Musulmi a fadin Nijeriya da ma duniya baki-daya.

Dakta Bichin, ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da Fefan Karatun Alkur’ani mai girma wanda Malama Gwana Nafisa ta raira kira’a, aka kuma kaddamar a gidan tunawa da Marigayi Mallam Aminu Kano da ke Unguwar Gwammaja cikin Birnin Kano, ranar Lahadin da ta gabata.

Bikin kaddamar da fefan, ya samu halartar manyan baki irn su mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar na uku, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi 11, sai kuma Sardaunan Kano kuma Dan Majalisar Dattawa, mai wakiltar Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau.

Haka zalika, kowannansu ya sayi kwafin wannan Fefan Karatun Alkur’ani kan kudi Naira Milyan daya-daya tare da yaba wa wannan mata Mahaddaciyar Alkur’ani mai girma tare da yi masa hidima.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai ta kasa reshan Jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khalil ya bayyana cewa, akwai bukatar a taimakawa irin su Gwana Nafisa, domin cigaba da amfanar da al’umma da wannan baiwa da Allah Ya yi musu na ilimi, musamman ilimin mace ilimin  al’umma ne baki-daya.

Haka nan, ita ma a nata jawabin, Malama Gwana Nafisa Yusuf Bichi ta bayyana cewa, yanzu babu abinda ta sanya a gaba kamar koyo da kuma koyarwa a rayuwarta, sai kuma burinta na kafa babbar makaranta domin koyar da yara maza da mata Matasa, kai har ma da manya wannan karatu na Alkur’ani mai girma da kowacce kira’a da ake da ita a ilimance.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: