Connect with us

Bakon Marubuci

Tabarbarewar Lamura A Garin Sammakal

Published

on

Garin Sammakal dai ya kasance wani hamshakin gari ne da ya wanzu cikin wannan Nahiya tamu ta Afurka, kusan sama da Shekaru dari biyu (200) da suka gabata.

Wancan gari na Sammakal, wasu lokuta, na da kamanceceniya ainun da Kasashe irinsu Najeriya, Niger, Cameroon, America, China da sauransu ta fuskoki da dama. A daya hannun kuwa, ya yi hannun riga ne da su.

Hakika, Allah Madaukakin Sarki, ya azurta wancan gari na Sammakal da dimbin miliyoyin al’uma kusan miliyan dari uku (300m). Sai dai nasu yawan, bai zamto irin na Kasar China ba, domin kuwa ba ya amfanarsu, sai suka zamto tamkar taron tsintsiya ne babu shara, ta fuskar amfanar da kai, da Kasa.

Akwai Kabilu kashi-kashi kusan dari biyar (500) a garin na Sammakal, sai dai maimakon su hade kawunansu wuri-guda, sai Turawan Yamma ke amfani da banbance-banbancen dake tsakaninsu, wajen gwara kawunansu, ta-kai ta-kawo ma, wasu Kabilun, na ta gwagwarmayar sai sun balle daga tarayyar zaman kasar da karfi da yaji. Maimakon su kara dunkulewa wuridaya su karo karfi tamkar Amurka, amma ina! Sun ki.

Addinin Musulunci da na Kiristanci ne manyan Addinan da suka mamaye sauran daukacin Addinai da ake da su a garin na Sammakal, sai dai akwai masu bautar Shaidan, da masu yin Tsafi, da masu yi wa Iskokai hidima, da wadanda suka rungumi Gumaka, duka a matsayin bauta. Wasu ko, Soye-soyen zuciya suka rika, kai har da ma wadanda suka riki Takalmi a matsayin abin-bauta a garin. Banbancin addinin da ya wanzu a garin, bai zamto rahama a gare su ba, ta yadda wanda ke kan turba ta daidai, zai ja batacce, ta hanyar kyakkyawar mu’amala da wa’azantarwa, Allah Ya ba shi lada. Maimakon haka, sai rikice-rikicen addini ya mamaye garin. Ta-kai ta-kawo ma, wani rikicin dake wanzuwa a tsakanin wadanda ke mabiya Addini guda, ta fi zafi sama da masu banbancin ra’ayin Addinin.

Akasarin Maluman mabanbantan addinai dake a wancan gari na Sammakal, shiryar da sauran mutane su fahimci gaskiya, ba shi ne muhimmi a gabansu ba, a’a, neman suna; abin hannun masu mulki; tara abin duniya da samun dimbin magoya baya ne abinda suka fi mayar da hankulansu a kai dare da rana.

Mawadata da masu mulki a wancan gari na Sammakal, babban abinda suka fi mayar da tunaninsu a kai shi ne, yaya za a yi na tara dukiyar yaki-haram yaki-halas tamkar Dan-Karuna?.

Raunana Talakawa, kwata-kwata ba sa cikin zukatan masu mulkin garin Sammakal da mawadatan cikinta. Iyalansu da kawalansu da sauran makusantansu ne kadai a kokon-zuciyarsu. Kowa ma ya mutu, amma ban da “yan lelensu.

Hasada ce babbar abar da ta cika zukatan miskinan garin Sammakal suntsir. Falala, ko wata wadatar da Allah Ya bai wa wasunsu, a kullum fatansu shi ne waccan ni’ima ta gushe, a dawo biyu-babu.
Akasarin Talakawan garin na Sammakal kam jahilai ne murakkabai, shi ya sanya a kullum wasu masu mulki, da wasu maluma da wasu daga jagororin kabilarsu, ke amfani da su, wajen cimma muradansu, ko da kuwa za ta kai su ga daukar rayukan ‘yan-uwansu raunana ne. Saboda tsantsar jahilci da yai wa talakawan garin Sammakal katutu, ba sa iya tsallake tayin-naira, wajen aikata kowane irin danyen aiki ne, ko da kuwa ya saba da hankali ne, ko wata koyarwar addini, wannan abin da za a nemi su aikata su amshi dala, a shirye suke da su aikata shi. Wannan dalili kam, ya taimaka gaya zuwa ga kyankyashe makasa da sunan Addini, ko ka kira su da ‘yan-ta’adda; samar da masu garkuwa da mutane, sai an kawo kudin fansa; yawaitar matsafa dake layya da rayukan jama’a; kirkirar ‘yan bindiga dadi, da sauran tsinannun bayi, wadanda kashe Kadangare, ya fiye musu wahala a kan kashe Mutum, babba ne ko yaro.

Bugu da kari, cikin wancan gari na Sammakal, akwai Kungiyoyin al’uma birjik, da sauran Kungiyoyin dake riya kwato hakkin masu rauni, yau da gobe, sun birkice zuwa ga neman Daloli wajen Turawan Yamma, a matsayin babbar manufarsu abar nema, tare da rikidewa zuwa ga Kungiyoyin iza-wutar KABILANCI a Kasa.

Gidajen Rediyo da na Jaridu a garin na Sammakal, babu wani abu da suka fi mayar da hankalinsu a kai, sama da kare muradan wadanda suka samar da su. A wasu lokutan, sukan dan sirka da kishin-kasa cikin aikin, sai dai ba shi ne hadafin akasarinsu ba. Da yawa cikin wadancan kafofin sadarwa a garin na Sammakal, sun sunkuci rigunan kabilanci sun yafa a jikinsu.

Alkalanci da Lauyanci a wancan gari na Sammakal kuwa, ba tsantsar kare gaskiya ko iya yakar karya ne ba abin-birgewa, sama da samun makudan kudade, samun tarin alfarmomi, a wajen masu mulki da mawadata a Kasar. Saboda wancan dalili, sai ya zamana cewa, samun adalci ko samun rinjaye a Kotunan Kasar Sammakal, ya danganta da karfin aljuhunka ne!!!

Jami’an tsaro ma a Kasar ta Sammakal, ba da sama ne suka fado ba, su ma halinsu, sammakal yake da na al’umar Kasar ta Sammakal. Kare rayukan jama’a, ba shi ne muhimmi a gaban akasarin jami’an tsaron garin Sammakal ba, face samun kudi a duk sa’adda aka tura su aiki. Da yawansu, an sha samunsu da laifin bindige mutum, kawai, saboda ya hana su cin-hancin kudi, daga Naira Ashirin zuwa Naira Dari Biyu kacal. Su kashe mutum, tamkar sun kashe kiyashi ne, kai!!!!! wata shari’ar kam sai dai a Lahira!!!.
Babu wadatattun shafukan da za a fede duka munanan halayen da suka bayyana karara a zahiri cikin wancan gari na Sammakal, lokacin da iya-shege ke kilisa gabanin dulmiyewar garin zuwa ga KUNCIN RAYUWA. Saboda hatta zamantakewar aure a garin, ba ta yin dadi, muddin Maigida ba shi da abin duniya. Sannan, a sau da daman lokuta, za a ga suma akasarin mazajen garin, ba suna yin aure ne ba a matsayin ibada, face sai don a ci duniya da tsinke. A sami kyakkyawa ta fita taro. Ba safai ne ba a garin Sammakal, za a ga mutum ya damu da tarbiyyar gidan su matar da yake hankoron aura. Kawai shi, idan wasu halittu na jikinta suka kwanta masa a rai, shikenan, ya sami masoyiya. Ya sami gimbiya. Ya sami MATAR AURE.

Zaman munafurci a gefen hanya, gidajen biki da sauran Majalisai, na daga ababen da jama’ar wancan gari na Sammakal suka fi mayar da hankali, manyansu da yaransu.

Da yawan marubuta da masharhanta a wancan gari na Sammakal, ba suna yi ba ne don neman yardar Allah, a’a, a na yi ne, ko dai don a birge, ko don kabilanci, ko don gambara, ko uwa-uba don a sami kudi, ba don begen gyaruwar al’amura ba ne ba a Kasa.

A taikaicen takaitawa dai, bayan miyagun halaye sun game daukacin sako da lungu na wancan gari na Sammakal, sai aka jarrabi jama’ar Kasar da wani irin mummunan talaucin da hatta mutum mai Shekaru hamsin (50) a Duniya, zai ce maka bai taba yin tozali da irin waccan fatara ba. Ya faru a da daman Kasashe gabanin garin Sammakal, masana kan tashi haikan ne wajen shiryatar da jama’ar Kasa, yayinda abubuwa suka doge tabarbarewa, amma ban da garin Sammakal, domin kuwa, hatta yaran da ake tura wa Malamai Makarantu, don su ilmantar da su, sai suka buge da banka musu cikunan shege.

Talaucin da ya afkawa mutan Sammakal kuwa, ta-kai ta-kawo cewa, wadanda ba sa samun sukunin cin-abinci sau biyu a rana a garin, sun rinjayi masu ci sau uku a rana. Kai! akwai ma wadanda ke ci sau guda daya ne jal a Kasar ta Sammakal.

Samun ilmi ma ya gagara a garin, sai idan kana da kudi, koko, wani mai kudin ya tsaya maka.

Da yawan marasa lafiya a garin, sun ta mutuwa ne, saboda rashin kudin sayen magani. Da yawan marasa lafiya, wadanda ba su da abin sayen magani, sai suka koma yin bara a kan tituna da kafafen yada labarai, suna masu neman-dauki daga mawadata.

Mummunar makoma da mutanen Sammakal suka tsinci-kansu, bayan tabarbarewa ko gurbacewar halayensu, ba su fita daga ita ba, har sai da kowa ya koma da baya, ya sake tunani, ya je makaranta, sannan ya koma aikata daidai, bayan tuba wajen Mahalicci Allah, sai gashi an wayigari, mamakon arzikin Kasar ta Sammakal ya dawo. Al’amura suka kyautata. Rayuwa ta yi dadi, aka daina yin kashe-kashen jama’a na ba gaira-ba-dalili. Doka da Oda suka zauna. Adalci ya mamaye Kotunan Kasar.

A takaice, sai da Kasashe masu tarin yawa suka tsallako cikin waccan Kasa ta Sammakal, suka kwaikwayi hanyoyin da suka bi, suka dawo cikin Ni’ima Mayalwaciya.

A Shekarar da abubuwa suka kyautata ne cikin waccan Kasa ta Sammakal, wata Jarida da ake kira da Kukan Kurciya…, wadda Malam Jere ya samar, ta fito, ga abinda ke rubuce a shafin farko na jaridar;

“…Babu shakka, muddin jama’a na son ganin daidai cikin lamuran rayuwarsu ta yau da kullum, sai kowa ya tsaya inda ya kamata ya tsaya. Sai an kawar da hadama da son danne hakkin mai rauni. Sai an shimfidar da adalci a Kasa sama da alfarma ko yunkurin zaluntar wani. Sai mutane sun koma makaranta, sun yi karatu mai kwari. Uwa-uba, kowa ya rika yin abu, ba don komai ba, sai don son haduwa da Allah lami-lafiya ba don jama’a su yi masa jinjina ba…”.

Idan kuwa haka abin yake, mai zai hana ne Najeriya ta koma da baya, ita ma ta yi koyi da Kasar Sammakal?
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: