Connect with us

LABARAI

Mahautan Oko-Oba Da Ke Legas Sun Yi Taron Hadin Kai

Published

on

Mahautan mayankan Oko-oba da ke Legas sun yi babban taro domin karin hadin kansu don ci gaban wannan sana’a tasu.

Sailin da yake jawabi ga taron ‘yan jaridu, Shugaban Kungiyar Hadin Kan Mahuta kuma Galadiman Yamma da ke Legas, Alhaji Umar Adam, ya nuna farin cikinsa da yadda ya ga shugabannin mahauta na sassa daban-daban da suka amsa wannan kira da aka yi masu don cigaba da hadin kai da zaman lafiya.

Galadiman Yamma ya kara da cewa kowa ya rike sana’ar sa ta fawa hanu biyu-riyu sannan ya yi kira ga al’umma su sa tsoron Allah a zukatansu. “kuma mu yi kokari mu zauna da abokan sana’armu lafiya, kuma m ubi dokokin kasa, da jIhar Lagas da karamar hukuma don mu zauna lafiya a wajen neman abincinmu,”.

Ya yi adu’ar fatan alkhairi ga daukacin al’ummar wannan gida namu maitarin albarka na gode.

Shi kuma a nasa jawabin, Sarkin Fawan Oko-oba da ke Legas, Alhaji Usaman Ustaz ya baiyana wannan taro da cewa rana ce ta farinciki kuma mai dauke da tarihi na farinciki ganin yadda mahauta suka yi dandanzo a wannan wuri domin karin hadinkai da cigaba,

“A yau farin cikin da nake da shi na wannan taro ba zai musaltu ba, ga yayyena suna zaune da sa’o’ina a zaune ga kannenna ga kuma ‘ya’ya har mu da iyayen gidansu fulani a zaune, saboda haka ina kara godiya ga Allah da na ga wannan rana ta hadin kan mahauta”.

Ya kuma roke su su bawa marada kunya kuma ka da su samu kofa ta raba kawunansu, sannan ya yi kira da a zauna lafiya da abokan kasuwanci domin sai da hadinkai ake samun ci gaba.

Daga cikin shugabanin da suka halarci taron akwai shugaban Kungiyar Mahuta ta Kasa, Alhaji Samaila Ibrahim da Shugaban Arewa Irepodun Butcher And Market Association Alhaji Abdulhadi Ibrahim da Babban Sakataren Kungiyar Jigawa Butchers Association Ubale Isah Umar da Shugaban Internation Butchers Association Alhaji Ado Kowa A Bashi da Shugaban Hausa Community Butchers Association Alhaji Ibrahim Dan Kasa da Shugaban Arewa Muna Tare Alhaji Umaru Gwarzo.

Daga cikin manyan baki da sukai jawabi Babban Sakataren Enchy Butcher Association Of Nigeria, Ya’u Saidu Yakubu ya yi farinciki da jin dadin wannan hadinkai da aka samu, kuma ya baiyana cewa kofa a bude take domin karbar shawarwari daga kowanne bangare domin samun ci gaba mai dorewa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: