Connect with us

RAHOTANNI

Tataccen Bayani A Kan Cutar Coronavirus A Mahangar Musulunci

Published

on

Babban Malamin addinin Musuluncin nan, Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya ja hankulan al’ummar Musulmi dangane da cutar Cobid 19 da ta addabi duniya a halin yanzu.

Babban Malamin ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamu Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano, inda ya yi bayani a takaice cewa, zan yi amfani da wannan dama kafin mu fara karatu domin tunatar da ‘yan uwa Musulmai a kan ya-nayin da duniya take ciki a halin yanzu na afkuwar cutar nan da ake kira da (Corona Birus).

Mu duba mu gani yadda wannan ‘yar karamar kwayar halitta ta cuta, wadde ko da abin hangen nesa (Microscope) sai an kura ido sosai ake iya ganin ta, amma gashi ta ma-yar da kowa gida, ta tayar da hankalin duniya, har kasashe masu tinkaho da karfin kimiyya da karfin tattalin arziki, da ci gaba. Hankulansu ya tashi, Lissafinsu ya birkice, duk wani abu da suke tinkaho da shi bai iya amfanar da su komai ba, wanda wannan lallai shi zai nuna maka karfin ikon Allah, kuma zai nuna maka babu wani wanda ya isa gaba ga Allah.

Mu al’ummar Musulmi ga matsayar da ya kamata mu dauka dangane da wannan cuta:

(1) Kallon da musulmi ya kamata su yi wa wannan cuta daban yake da na kafirai, haka a cikin musulmai din ma, mai karanta Alkur’ani da Sunnar Annabi (S.A.W) kallon da zai yi mata daban yake da na wanda ba ya karanta su. Mu musulmi mun yi imani da kaddara, duk wani abu da ya faru, to dama can Allah Ya san da shi, kuma bai faru ba sai da iznin Allah, saboda babu abin da ke gudana a cikin Mulkin Allah sai da saninsa. Malamin ya ambaci ayoyin Alkur’ani mai girma a kan haka.

(2) Mu Musulmi mun sani cewa, ba wannan ne farau ba, ba yanzu aka fara samun irin wannan annoba ba, Allah Ya sha aiko da azabarsa ga al’ummomi da suka gabace mu, saboda sun kangarewa tafarkinSa, sai Allah Ya aika musu da annoba iri daban-daban, misali: mutanen Fir’auna, Allah Ya aika musu da annoba iri-iri, kamar annobar ambaliyar ruwa, annobar jini, duk abin da suka bude sai suga ya zama jini, annobar fara da kwarkwata. A karshe kuma Allah Ya halakar da su. Haka mutanen Annabi Nuhu kafinsu, Allah Ya aiko musu ambaliya ya halakar da su, haka mutanen Annabi Lud Allah Ya kifar da su suka halaka baki daya.

(3) Duk da cewa ita wannan al’umma ta Annabi (S.A.W) Allah Ya yi alkawarin ba zai tumbuke ta Ya halakar da ita baki daya ba, idan da Allah Ya so haka din tabbas zai iya, irin wadannan musibu sun isa shaida a kan haka, to amma Allah sai ya aiko da irin wannan annoba domin jan kunne da kashedi ga bayi. Yayin da annobar ta zo kuma ba ta banbance salihi nagari da na banza, kowa hadawa take da shi, sai dai tana zama Rahama ga Salihai, azaba kuma ga fandararru.

(4) Daga cikin darasin da ya kamata musulmi ya lura dashi a kan sha’anin wannan cu-ta, mu duba mu gani, a lokacin da Dan’adam yake tutiya, yake tinkaho cewa ya mallaki ilimi, ya mallaki karfin tattalin arziki, wasu har suna ganin Allah ma baya yi musu ko-mai, su sun isa, su sune. Kwatsam sai ga wata ‘Yar karamar halitta daga halittun Allah, wacce ido ma baya iya ganinta saboda tsabar kankantar ta, sai gashi ta baza duniya, ta bazama manyan kasashe, tattalin arziki yana ta rushewa, kowa ya firgita. Lalle wan-nan ya isa wa’azi! Wannan ya isa shaida akan girman Allah da karfin mulkinsa.

(5) Mu musulmi mu sani cewa babu abin da zai yaye mana wannan annoba illa kadai mu koma ga Allah, mu guji dukkan abubuwan da ke janyo Allah Ya yi haka ga al’um-ma, kamar manyan laifuka, Zinace-zinace, Zalunci, barna a bayan kasa.

(6) Mu sani cewa komawa ga Allah shi ne matakin farko domin magance wannan an-noba, duk wani abu da ba wannan ba ciko ne, amma komawa ga Allah shi ne Jigo. Mu koma ga Allah da yin addu’oi da yawaita istigfari.

(7) Mu sani cewa, lalle babu wata musiba da ta wuce a jarrabe ka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe masallatai, ana hana fitowa Sallar Jam’i, har Sallar juma’a da yawa daga kasashe sun bayar da sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta. Lalle wannan abin tsoro ne, kamar Allah Ya yi fushi da mutane ne ya ce: Ku fita ku bar min dakunana Masallatai tunda barnar ku a bayan kasa ta yi yawa.

Babbar musiba ce, a rabaka da dakin Allah, a ce babu Umarah, babu Dawafi, babu Sallarjam’i, lalle babu musibar da tafi irin wannan musiba a cikin addini. Tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba gare shi.

(8) Musulunci ya yarda da tsarin killace marasa lafiya, da kuma tsarin kare kai daga cututtuka, musulunci shi ya fara zuwa da irin wannan tsari. Haka zalika, Malamin ya ambaci Hadisi a kan haka, amma kuma a musulunci mun yi imani da cewa zama da mai cuta ba shi ke janyo kamuwa da cuta ba, har sai idan Allah Ya hukunta haka, cuta a karan-kanta bata da ikon shiga ta yi tasiri a jikin mutum sai da ganin damar Allah. Ita cuta sababi ce, sababi kuwa baya aiki a karan-kansa sai idan Allah Ya kaddara, mu duba mu gani, wuta a al’adarta tana kona mutum, amma Annabi Ibrahim da aka jefa shi a wuta sai Allah Ya sa wutar taki kona shi, mu duba ruwa yana dulmiyar da mu-tum, amma sai Allah Ya sa Annabi Musa da mutanensa suka taka saman ruwa suka wuce ba tare da sun dulmiya ba, saboda haka ko da abu sababi ne, Allah Yana iya zare sababiyyar yaki yin aiki.

A musulunci mun sani cewa duk abin da ya same ka ba zai kubuce maka ba, duk ku-ma abin da ya kubuce maka ba mai samunka bane. Kamar yadda Annabi (S.A.W) Ya fadawa Abdullahi Dan Abbas.

(9) irin wannan annobar an sha yinta a baya, a lokacin Sahabbai, an samu annoba da ta yi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin Sahabbai, kamar: Mu’az bin Jabal, da Abu Ubaida bin Aljarrah da sauran su, wannan ya faru a shekara ta (18) bayan Hijra. Haka nan akwai annobar da aka tabayi inda tayi sanadiyyar mutuwar ‘Ya’yan Anas bin Malik kusan mutum saba’in (70), da ‘Ya’yan sahabi Abu Bakrata kusan Mutum arba’in (40).

(10) Ya na daga cikin abin da zai magance irin wannan annoba, gujewa aikata Zalunci, danne hakkin mai hakki, wajibi ne shugabanni su rika yin adalci su guji yin zalunci, domin zalunci sababi ne na afkawa irin wannan masifa. A karshe Malamin ya yi addu’a mai ratsa zukata, inda Ya roki Allah da Ya yaye mana wannan masifa ba don halinmu ba, Allah Ya dube mu da Rahamarsa da Ludufinsa ya kawo mana agaji.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: