Connect with us

WASANNI

Gasar Wasannin Makarantu Na Maltina Ta Wuce Zakulo Sababbin Zakaru Kadai

Published

on

Bayan samun dimbin nasarorin da kuma yakinin da kamfanin da ke sarrafa Maltina ya ke da shi akan daukacin malaman makarantu dake a fadin Nijeriya, a karkashin shirin kamfanin na Maltina na malamin shekara ya sake samar da wani tagomashi ga zaukacin daliban dake a makarantun fadin kasar, inda a kwanan baya sanannen kamfanin na Maltina, ya gabatar da wasanni na makarantu.

 

Wasannin na makarantun na kamfanin Maltina shine dauki na kwana-kwanan da da ya samar a daukacin fadin kasar.
Har ila yau, wasannin sun hada da, gasar guje-guje da yin gasa a tsakanin makarantu don fitar da zakaru a makaratun sakandare dake a fadin Nijeriya.
Kusan shine karo na farko kuma an kirkiro dashi ne don samar da dauki data mutuwar al’adar yin wasannin a makarantun dake a Nijeriya, musamman don taimakawa wajen zakulo hazikan yan wasa da ake kira manyan gobe.
Bugu da kari, an tsara wasannin na kamfanin Maltina ne a tsanake don ciyar da rayuwar yara gaba da kuma fito da bajintar su a fili ta hanyar wasanni don a kara masu kwarin gwaiwa.
A daukacin fadin duniya, harkar wasannin da ilimin zamani, sun kasance hanyoyin tsamo kai daga cikin kangin talauci, inda shirin na gasar wasanni na kamfanin na Maltina, ana da bukatar sa matuka, musamman don samar da cigaba.
Gasar ta wuce kawai shiyawa daliban da suka fito daga makarantu, inda gasar ta kamfain na Maltina ta nuna cewa, babu wata tantama kamfanin yana taimakwa wajen hada kan nahalartan wasan, zakulo da hazikan yan wasa, inda zasu kai har zuwa zagaye na karshe bayan fafatawa da takwarorinsu.
Saboda sha’awar da yaran su ke da ita wajen shiga cikin gasar wasannin ta makaratun, gasar wacce ba a jima da kammala ta ba, ta samu halartar makaratu da dama, inda yan jihar Lagos ne suka fi shigarta.
Jihar Lagos ta na da makaratu mahalarta su 182 da su ka fito daga shiyoyi shida, inda kuma makaratu guda 120 su ka fito dsga jihar Kano, jihar Anambra na da makarantu 124 Abuja na da makarantu guda 116 da su ka yi rijista don shiga gasar.
Daga cikin sama daliban makarantu miliyan 20 wadanda suka shiga gasar da kuma wadanda ba su shiga ba, sunan Ojo yar shekara 17 ce ya fi yin tashe.
Ojo ta fito ne daga babbar makarantar da ke rukunin gidaje na Ijaye, inda ta zamo babban zakara a gasar tsere bayan ta lashe tsare na tsawon mita 100 da kuma na mita 200 tare da samun karin lambar Zinare.
A bisa wannan garumin kokarin nata, Ojo ta samu gurbin karo karatu a dukkan Jami’ar Tarayya da ta ke bukata ta hanyar kamfanin na Maltina.
Babu wata tantama haka ya sanya Ojo ta nuna hazaka a jihar Lagos abinda ta ke bukata na daukaka matarbar guge-guje har zuwa fadin dunuya nan bada jimawa ba.
Baya ga Ojo, wasu hazikan yan wasa sun yi nuni da cewa, irin wanna gasar za ta taimaka wajen kare fannin wasannin daga dukushewa a kasar nan.
Ta ce, kamfanin na Maltina, ya yi namijin kokari wajen samar da damarmaki a jihar inda har wasu yan makaranta a jihar suka kai wani mataki kuma muna fatan sayran suma zasuyi koyi domin har yanzu, akwai hazikan yan wasa da ba’a iya zakulo su a kasar nan ba.
Wani jami’i a ma’aikatar ilimi ta jihar Lagos Tayo Adewale ya sanar da cewa, dan wasan tsere da yafi kowa gudu a Nijeriya Seye Ogunlewe shima ya fito don karawa yan wasan kwarin gwaiwa a wajen gasar.
Kamfanin na Maltina, ya taka muhimmiyar rawa wajen zakulo hazikan yan wasa mata da maza.
Ba kamar a shekaru na na baya ba, inda kawai muke shiga gasar dakunan karatun dalibai ba da kuma a wani ake gayyatar makarantu zuwa yin gasar guje-gujeta da tseren makaantu ba.
Amma daga wannan damar da kamfanin na Maltina ya samar, zata kasance daya daga cikin samar da damarmaki ga matasa.
Hukumar wasannin makarantun ta kasa (NSSF), ya zama wajibi ta tabbatar da hada irin wannan gasar, ya kasance an gudanar dashi a cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda kamfanin zai samu sukunin cigaba da bayar da gudunmawar sa wajen gudanar d gasar.
Gasar ta makarantun ta Maltina, babu wata tantama ta samar da kafar wayar da kai kan wasanni a Arewacin Nijeriya, idan akayi la’karinda yadda aka halarci gasar, inda a ka gudanar da gwajin zagaye zuwa na karshe a jihar Kano.
Har ila yau, taron gasar ta wanannin ta nuna karo na farko, inda kuma yan gasar, za su hadu da abokan fafatawar su da suka fito daga wurare daban-daban daga kasar a inda su ka hadu a jihar Lagos don zuwa zagaye na karshe na gasar.
Babu wata tantama, gasar wasannin suna kuma taimakawa wajen kara hada kai da kuma dankon zumunci a tsakanin miliyoyin matasan da ke a kasar, musamman idan a ka yi la’kari da dukkan wanda ya halarci gasar, akwai labarin da zai sanar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: