Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sin Na Taimakawa Wajen Samar Da Kayayyakin Yaki Da COVID 19 Ga Kasa Da Kasa

Published

on

Cutar COVID 19 na yaduwa a duk fadin duniya, a halin da wannan kalubale ya daibaibaye kasa da kasa, Sin na tallafawa kasashen duniya ba tare da bata lokaci ba bisa tunanin raya kaykkaywar makomar Bil Adam ta bai daya.

Yayin da aka samu mutane 3 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Zimbabwe, ta hannun Tarayyar Afrika (AU) ne, kasar ta karbi kayayyakin gwaji 20,000 da makarin baki da hanci 100,000 da rigunan kariya da makarin fuska guda 1,000 da za su taimaka mata yaki da cutar, daga hannun hamshakin dan kasuwar kasar Sin wato Jack Ma.
A wannan rana kuma, shugaban tawagar jakadun Sin dake AU, Liu Yuxi, ya gana da jami’a mai kula da harkokin jama’a na AU, Amira El Fadil, inda suka rattaba hannu kan wata takardar shaidar karbar na’urar gwada kwayar cutar, wanda shi ne karo na biyu da Sin ta tallafawa nahiyar Afrika.
Amira El Fadil, ta gode da tallafin kayayyakin jinyya da gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na Sin suka baiwa nahiyar. Ta ce, Sin sahihiyar abokiya ce kuma ’yar uwar Afrika. Ta ce nahiyar na fatan kara hadin kai da kasar Sin ta fuskar yakar cutar da koyon fasaha da dabaru masu inganci daga wajenta.
Da safiyar jiya Talata, agogon Hungary, kayayyakin kandagarkin cutar da kasar ta saya daga kasar Sin, suka isa filin saukar jiragen sama na Budapest, fadar mulkin kasar, inda firaministan kasar Viktor Orbán ya tarbi ma’aikatan jirgin a filin saukar jiragen sama na birnin. (Masu Fassarawa: Fa’iza Mustapha, Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: