Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Babu Noman Da Ya Kai Na Masara Sirri – Shugaban kungiyar Manoma

Published

on

Shugaban kungiyar Masu Noma Masara na kasa reshen Jihar Kano, Alhaji Garba Munkaila, ya bayyana noman masara a Nijeriya a matsayin wani abu mai sirrin gaske tare da falala a cikinsa, har da ma dukkanin wasu wurare da ake noma ta a fadin duniya.

Don haka a cewar tasa, duk Manomin da ba ya noman masara kamar yadda aka saba yi duk shekara, ko kadan bai san sirrin noma ba. Saboda haka, a matsayinmu na masu noman wannan masara; muna jan hankalin sauran ‘yan’uwanmu Manoma, su yi kokarin jarraba noman masara sakamakon dimbin alhairin da ke cikinsa.
Kazalika, ba mu ce ya bar noman da ya saba yi ba, amma dai ya yi kokarin jarraba noman masara ya gani, wata rana shi da kansa zai baiwa wasu irin wannan shawarar da muke ba shi. Alhaji Munkaila, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da mane ma labarai a Ofishin kungiyar da ke Kano, ranar Laraba da ta gabata.
Har ila yau ya kara da cewa, wannan kungiya da ke da rassa a kowace karamar Hukuma da ke Kano, tare da Shugabanninta a kanan Hukumomi 44 na Kano, sannan kuma kowace Mazaba akwai Ofishin kungiyar kamar yadda kungiyar ke da rassa a dukkannin jihohin kasar nan 36, ciki har da Abuja.
Haka zalika, a shekarar da ta gabata Manoman masara na wannan kungiya sun noma kadada akalla dubu 350, inda hakan ya kara tabbatar da cewa, ko shakka babu Manoman masara na taka rawar gani kwarai da gaske wajen bunkasa tattalin arziki tare da sama wa Matasa aikin yi a fadin wannan kasa Nijeriya baki-daya, in ji Shugaban kungiyar.
Har wa yau a cewar tasa, noman masara a halin yanzu ya zama na zamani ba kamar a lokutan baya ba, komai yanzu ya zama na ilimi da bin kaidoji, musamman ta fuskar yin amfani da magunguna da kuma shi kansa irin shuka da sauran makamantansu.
Kazalika, ya yabawa Ma
aikatar Gona ta Gwamnatin Tarayya, bisa bin umarnin da ta yi na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wajen baiwa Manoman masara ingantaccen irin shuka, magungunan kwari da kuma takin zamani, wanda hakan ya taimaka matuka gaya wajen kara bunkasa noman masara a Nijeriya.
Haka nan, batun rufe iyakokin kasa wanda wannan gwamnati ta yi, ya kawo alhairai masu yawan gaske musamman ga Manoma da ma sauran alummar Nijeriya baki-daya. Domin kuwa, hakan ya yi sanadiyyar samun Manoman masara da na shinkafa da sauran makamantansu masu yawan gaske, dalili kuwa komai ka noma yana da daraja a kasuwa. Don haka, muna kara yin jinjina tare da godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa wannan gata da ya yi mana a matsayinmu na manoma.
A karshe, Shugaban kungiyar Manoman (Maize Association of Nigeria), ya sake yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan hana shigo da masara da ya yi wannan kasa, musamman idan aka yi la
akari da yadda ake noma ta a fadin kasar. Ko shakka babu, Shugaban kasar ya yi kyakkyawan hangen nesa kwarai da gaske.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: