Wata kungiya mai rajin Samar da shugabanci nagari a dukkan matakai (C2G-Network), ta shawarci al’umm’ar Nijeriya su fito kwansu da kwarkwata domin zaben shugaba nagari.
Kungiya ta jaddada wa jama’a alfanun zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Dan takarar shugabancin Nijeriya a karkashin Jam’iyar APC, inda ta ce kudirinsa da alkawarrunkasa gaba daya, ya karkatashi zuwa taimakon ‘yan Nijeriya
A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Michael Musa da na sakatarensa, Ajayi olushola, sun bayyana cewa Tinubu ya cancanci a zabe ne saboda irin ayukan alherin da ya yi a zamanin baya da ya yi Gwamnan jihar Lagos
“Kungiyar C2G-Network ba ta da wata manufa, kawai dai ta yi zurfin tunani ne tare da tantance dukkanin yan takara shugaban kasar, sai aka dace kudirin yakin neman zaben na Asiwaju, ya fi yin daidai da jinkan al’umma.”
“Idan muka duba kudurorin da ya bayar na yakin neman zaben nasa, gaba daya, babu na biyunsa a ‘yan takara.
“Sa’annan Alkawarrukan da ya yi wa ‘yan Nijeriya duk masu yiwuwa ne, saboda haka, Tinubu ya cancanci a zabe shi”
“Ya yi aiki matuka a baya, kuma an gani,kowa ya shaida, a zamanin da yake Gwamnan Lagos a shekarar 1999 da 2007.”