Wani Lauya masanin tsarin mulki, Mista Kayode Ajulo, ya gargadi ‘yan siyasar Nijeriya da jam’iyyun siyasar kasar kan taka dokar zabe ta 2022, musamman dangane da gudanar da yakin neman zabe gabanin babban zabe na 2023.
Ajulo ya tunatar da ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a zabukan da ke tafe da cewa bisa ga tanadin dokar zabe, an sanya takunkumi da yawa don hana magudin zabe da aka saba shiryawa lokacin yakin neman zabe.
Lauyan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Laraba a Abuja, ya bukaci ’yan siyasa, jam’iyyu da sauran kungiyoyin yakin neman zabe da su kaucewa yakin neman zabe a fadar sarakunan gargajiya na fadin kasar.
Ya kara da cewa, Wuraren da aka ware don ibada, ofishin Jami’an Tsaro da gine-ginen gwamnati da aka ware don kula da jin dadin al’umma ba a yarda ayi yakin neman zabe a cikinsu ba.
Lauyan yace, duk wanda ya karya doka, Hukunci zai biyo baya, yayin da yake nakalto sashin da dokar zabe ta tanada, ya ce: “Sashe na 92 na dokar zabe, 2022, ya tanadi haramcin wasu ayyuka a yakin neman zabe.”