Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta barnata kusan shekaru takwas ba tare da cimma wasu abun a zo a gani ba.
Yayin da ya bayyana kusan shekaru takwas na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin asara, Atiku ya ce tabarbarewar mulkin jam’iyyar APC a kullum yana kara jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala a kullum.
- Ma’aikatar Tsaron Amurka Ta Fitar Da Rahoton Shekara-Shekara Kan Karfin Sojan Sin Da Nufin Fakewa Wajen Nuna Danniya Ko Babakere A Fannin Soja
- Tsohon Shugaban Kasar Sin Jiang Zemin Ya Rasu
Da yake jawabi a taron yakin neman zaben shugaban kasa a garin Akure a Jihar Ondo, na kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Yamma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya kara da cewa shekaru 16 da PDP ta shafe tana mulkin Nijeriya ba za a iya kwatanta ta da jam’iyyar siyasar shugaba Buhari mai mulki ba.
A cewarsa, “Ba za ku kwatanta abin da PDP ta yi a cikin shekaru 16 da abin da APC ta yi a cikin shekaru 8 ba, ba su tabuka komai ba.”
Yayin da yake nuna rashin aikin yi da talauci a fadin kasar nan, Atiku ya bayyana cewa gazawar gwamnati mai ci wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasa ya tabbatar da gazawar gwamnatin Buhari.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa idan jam’iyyarsa ta PDP ta samu nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2023, gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar nan da ake fama da shi.