Jam’iyyar APC ta sanar da nada gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Lalong, a matsayin daraktan gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2023 da ke tafe.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da yake hira da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa jim-kadan bayan sun yi wata ganawa da shugaba, Muhammadu Buhari, a Villa da ke Abuja.
- Atiku Da Tinubu Sun Fara Cacar Baki Kan Zaben 2023
- Tinubu Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba, Ya Tsufa, Cewar Surukinsa Tee Mac
Adamu wanda ya samu rakiyar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin dan takarar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da shi kansa gwamnan Jihar na Filato, Lalong.
Shugaban ya kuma sanar da nadin karamin ministan Kwadago, Festus Keyamo a matsayin jami’in watsa labarai na rikon kwaryar da kuma fitacciyar marubuciya a jiridar LEADERSHIP, Hannatu Musawa, a matsayin mataimakiyar Kakakin yakin zaben dan takarar APC.