Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa cewa ya yi alkawarin marawa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, baya a takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.
Daya daga jaridun Nijeriya ta ruwaito a ranar Asabar din da ta gabata, cewa Atiku ya yi alkawarin mara wa Wike baya a 2027 a matsayin wani sharadi na tabbatar da goyon bayan gwamnan Ribas ga takararsa ta shugaban kasa a 2023.
Sai dai yayin da yake mayar da martani a ranar Asabar, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya ce babu wani lokaci da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya yi irin wannan tattaunawa da Gwamna Wike ko wani.
Melaye, ya kara da cewa, labarin da ya fito daga wata jarida mallakin abokin hamayyar Atiku kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana sosai kan manufar Jaridar.
“Ina mai tabbatar muku cewa, babu irin wannan tattaunawa tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike na Jihar Ribas, babu wani lokaci Atiku Abubakar ya tattauna da Gwamna Wike.
Melaye ya ce “Atiku bai taba yin alkawari ko tattauna wa kan zaben 2027 da Gwamna Wike ko wani ba game da wannan batu. Ya kamata ku gane.”