Shugaban Hukumar Zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da cewa, Hukumar na kan gudanar da aiki domin ta wallafa sunayen wadanda ta yi wa rajistar katin jefa kuri’a kafin zaben 2023.
Ya sanar da hakan ne a taron masu ruwa da tsaki don yin dubi ga baiwa ‘yan gudun hijira da ke zaune a sansanin su da ke a Abuja damar yin zabe a 2023.
Yakubu ya ce, cikakken sunayen zai hada da sunayen sabbin masu jefa kuri’a da aka yi wa rajistar samun katin zabe, inda za a hada sunayen cikin wadanda aka yiwa rijista sama da Mutum miliyan 84.
Ya soki ikirarin da Kungiyoyi masu zaman kansu suke yi na cewa, hukumar ba ta shirya wallafa sunayen masu jefa kuri’ar ba.
Shugaban ya kuma baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, hukumar za ta wallafa daukacin rajistar mazabu guda 8,809 da ke a kanan hukumomi guda 774 kamar yadda dokar zabe da aka sabunta ta 2022 ta tanada.