Kungiyar masu karbar Fansho ta kasa (NUP) ta lashi takobi a zaben 2023 na shugaban kasa da kuma na gwamnoni ba za su zabi wadanda ba zasu mayar da hankali kan hakkokinsu ba.
Shugaban kungiyar na kasa, Godwin AdumisI, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abuja, inda ya yi nuni da cewa a kasarnan an jima ana mayar da su saniyar ware a kan hakokinsu.
Ya sanar da cewa, har yanzu muna ci gaba da sa ido a kan ‘yan takarar kuma da zarar lokaci ya yi zamu sanar da ‘ya’yan kungiyar da ‘yan Jarida wanda zamu zaba a matakin shugaban kasa da na gwamnoni.
Don haka mddin muka tabbatar da wadanda suke son a zabe su amma ba zasu mayar da hankali a kan hakkokin mu ba, za mu sheda wa, ‘ya’yan kungiyar da ‘yan uwanmu kar su kuskura su zabe su.
Ya kuma koka kan yadda wasu gwamnonin suka ki bin umarnin biyansu hakokinsu tare kuma da kin sabunta masu kudadensu duk da cewa, an samu sabon karin na biyansu kudadensu na fansho, inda ya kira ga gwamnatin tarayya da ta tilastawa gwanoni domin su biya su hakkokinsu.