Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, sun ce barazanar da gwamnan Jihar, Nyesom Ezenwo Wike ke yi ba za ta ba su tsoro ba.
Sun kuma sanar da goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, duk da cin zarfinsu da da kuma barazanar da ake yi musu ta kama su bisa umarnin Wike, hakan ba zai tsorata su ba.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Wa Dan Takarar Gwamnan YPP Hukuncin Daurin Shekaru 42 A Akwa Ibom
- Kungiyar Mata ‘Yan Jarida Ta Yi Sabuwar Shugaba A Kebbi
Daraktan kwamitin yakin neman zaben, Dakta Abiye Sekibo ne, ya sanar da hakan a garin Fatakwal a lokacin wata ganawa da wata kungiyar dattawan da ke goyon bayan PDP a garin Ogoni.
Sekibo, ya shawarci daukacin al’ummar jihar da su yi watsi da irin mulkin kama karya da Wike ke yi wa al’ummar jihar su kuma goyi bayan takarar shugaban kasar PDP, Atiku Abubakar ke yi na neman shugabancin kasar nan.
A nasa jawabin, daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar, Celestine Omehia, ya ce, rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, tuni an samar da mafita.
Celestine, ya kara da cewa a kowace irin zuri’a, dole ana samun sabani daga baya kuma a zama daya.
A cewar Celestine “A yanzu mun ci gaba kuma rikicin cikin gida a PDP, a yanzu ya riga ya wuce.”