Yayin da ya rake kasa da kwanaki 100 a gudanar da babban zaben 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ta tanadi takardun jefa kuri’a na shugaban kasa guda miliyan 187, domin shirin zabe zagaye na biyu idan hakan ta kama.
Kakakin hukumar INEC, Festus Okoye shi ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja.
- Zamanintar Da Sha’anin Gona Da Kauyuka Ya Dogaro Da Halin Da Ake Ciki Da Muradun Jama’a
- Nnamdi Kanu Ya Maka Gwamnatin Tarayya A Kotun Koli
Oke ya ce ‘yan Nijeriya miliyan 93.5 ne za su yi zabe, amma INEC ta rubanya takardun jefa kuri’a har suka kai miliyan 187 ko da za a kai ga yin zabe zageye na biyu idan ba a samu wanda ya lashe zaben ba a farkon lokaci.
Ya ce a bisa al’adar hukumar INEC tana irin wannan shirin a duk lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa tun daga shekarar 1999.
Okoye ya ce za a fara amfani da takardun jefa kuri’a miliyan 93.5 ne a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa, yayin da sauran takardun jefa kuri’a miliyan 93.5 an tanade su ne domin shirin gudunar da zabe zagaye na biyu idan har babu wanda ya yi nasara a zagayen farko.
Kakakin ya ce hukumar ta yanke hukuncin buga takardun jefa kuri’un miliyan 187 na shugaban kasa ne, domin zai yi mata wahala ta buga kuri’un cikin karamin lokaci.
Okoye ya ce, “A yanzu muna da jam’iyyun siyasa 18 da za su shiga cikin zaben 2023, sannan doka ta tanadi yadda za a tsayar da ‘yan takara har ma a samu wanda zai zama shugaban Nijeriya. Sakamakon karancin lokaci da doka ta bai wa hukumar INEC idan har ba a samu dan takarar da ya yi nasara a zagayen farko ba, sai hukumar ta dauki matakin buga kuri’un na zageye na biyu a lokacin da muke buga takardun zabe.
“Idan har ‘yan Nijeriya miliyan 93 za su yi zaben shugaban kasa, to za mu kara buga karin kuri’u miliyan 93 saboda zagaye na biyu idan har ba a samu wanda ya yi nasara ba.
“Daga karshe idan har ba a shiga zagaye na biyu ba, to hukumar INEC za ta lalata kuri’u miliyan 93 da ta buga saboda zagaye na biyu. Wannan yana faruwa ne saboda doka ya bai wa hukumar kwanaki 21 kacal wajen shirya zabe na biyu idan har babu wanda ya samu nasara a zagayen farko.”
Da yake bayyana yadda za a samu shugaban kasa da sharuddan da suka kamata na zabe zagaye na biyu, Okeye ya ce, “Sashi na 134 (2) na tsarin mulkin tarayyar Nijeriya wanda shi ne dokar kasa ya tilasta cewa wajibi ne duk wanda zai zama shugaban kasan Nijeriya ya fi sauran ‘yan takara yawan kuri’u. Kuma tilas ya samu akalla kashi 1/4 na kashi 2 bisa bisa 3 na kuri’un da aka kada a jihohi 36 ciki har da Abuja.
“Idan har babu dan takarar da ya samu yawan kuri’un da ake bukata, tsarin mulki ya tanadi cewa dole mu shirya zabe zagaye na biyu a cikin kwanaki 21. Ba dukkan ‘yan takara ba ne za su shiga zabe zagaye na biyu ba. ‘Yan takara 18 ne ke cikin takardun jefa kuri’a na zagaye na farko. Idan ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba, ‘yan takara guda biyu ne kacal za su shiga zagaye na biyu.
“Na farko shi ne wanda ya fi kowa yawan kuri’u, amma ya kasa samun akalla kashi 1/4 daga kashi 2 bisa 3 na yawan kuri’un jihohi ciki har da Abuja. Sai kuma na biyun wanda zai yi zagaye na biyun shi ne, ya zo na biyu wajen samun kashi 1/4 na kashi 3 bisa 4 na kuri’un da aka kada a jihohi da ciki har da Abuja.
“Dole ne mu buga kuri’un babban zabe da na zagaye na biyu a lokaci guda, domin haka hukumar INEC ta saba yi.”