Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya zabi Farfesa Kaletapwa Farauta, a matsayin mataimakiyar takararsa a zaben 2023, a jam’iyyar PDP.
Fintiri ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da abokiyar takarar ta shi a Yola a yau Laraba, inda ya ce Farauta, wacce a halin yanzu ita ce shugabar Jami’ar Adamawa, Mubi, an zabo ta ne bisa gaskiya, rikon amana, da kuma aiki tukuru.
- Matashiya Ta Rataye Kanta Saboda Auren Dole A Kano
- “Ku Ragargaji ‘Yan Ta’adda, Ba Sani Ba Sabo” —Shugaban NAF
Ya ce ana sa ran za ta iya sauke nauyin da za a dora mata tare da taka tsantsan da tsoron Allah, baya ga aikin da take yi na kula da gida a matsayin ta na uwa.
”An zabe ta ne sakamakon tunani da lissafi mai zurfi, musamman na bukatar tafiya da mata ta hanyar bai wa ko wanne jinsi hakkinsa,” in ji shi.
A nata jawabin, Farauta, wacce ta bayyana zaben nata cewa da ga Ubangiji ne, ta godewa Fintiri da kuma jam’iyyar PDP da suka zabe ta a matsayin wacce ta cancanta.
Ta tabbatar da yin aiki cikin biyayya, aminci, sadaukarwa da kuma tsoron Allah.
“Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara ga jam’iyyar a duk zabukan da za a yi nan gaba,” in ji ta.