Hankula sun karkata ga bukatar dakile rikice-rikice gabanin zaben 2023. Wajibi ne a dakatar da rikice-rikice gabanin zabe domin tabbatar da cewa zaben 2023 ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da wata matsala ba.
A makon da ya gabata ne, wasu magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar suka tsallake rijiya da baya, sakakon harin da ‘yan daba suka kai musu da adduna lokacin da suke kokarin lika allon yakin neman zaben dan takarar a karamar hukumar Omuma da ke Jihar Ribas.
- Ana Baje Kolin Shirye-Shiryen CMG A Taron Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa Karo Na Farko
- 2023: Za A Fara Shirye-shiryen Aikin Hajji Ranar 21 Ga Disamba – NAHCON
Da yake magana kan lamarin, kakakin kungiyar farar hula ta RIBSCO, Solomon Lenu ya yi tir da faruwar lamarin. Haka shi ma mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku a Jihar Ribas, Dakta Leloonu Nwibubasa ya yi Allah wadai da wannan ibtila’in, inda ya ce abun takaici ne irin wannan lamari yana faruwa a jihar.
Haka kuma wani lamarin ya afku, inda aka kai wa ayarin tawagar Atiku hari a Maiduguri da ke Jihar Borno a makon da ta gabata.
Kakakin yakin neman zaben Atiku, Sanata Dino Malaye ya daura alhakkin harin kan jam’iyya mai mulki ta APC a Jihar Borno, inda ya bayyana cewa sama da mutum 70 aka kwantar a asibiti.
“Sun yi kokarin hana mu gudanar da yakin neman zabe, kamar yadda nake magana a halin yanzu, akwai mutum 74 da aka raunata wadanda suke kwance a asibiti. Muna zargin jam’iyyar APC kan wannan lamari.
A cikin sanarwar da mashawarcin Atiku kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan daba dauke da tutar jam’iyyar APC suka farmaki ayarin tawagar motocin yakin neman zaben Atiku a Maiduguri.
A cewarsa, “Abun takaici ne wasu mambobin jam’iyyar APC a Jihar Borno su farmaki ayarin motocin yakin neman zabenmu a hanyar ziyara daga fadar Shehun Borno zuwa wurin gangaminmu. Dama mun san APC da irin wadannan muyagun dabi’u, inda a yanzu ne suka fara fitowa fili baro-baro.”
A cikin wadannan hare-hare guda biyu, APC ta nisanta kanta kan farmakin ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na PDP da ‘yan daba suka yi. Daraktan yada labarai na yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Bayo Onanuga ya yi zargin cewa, farmakin ya zo ne sakamakon rikicin da PDP ta samu a Jihar Borno, inda ya dage cewa APC ba ta da hannu kan wannan rikici.
Amma a cewar wani rahoto, wasu ‘yan daba ne suka jefi ayarin motocin Atiku lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi domin kai masa ziyara. Sai dai ba a bayyana jerin yawan wadanda suka jikkata ba lokacin da ‘yan daban suka farmaki ayarin motocin Atiku da duwatsu da sanduna da kuma sauran makamai.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Borno, Zanna Gaddama ya ce, “Gaskiya ne ‘yan daba da muke kyautata zaton ‘yan APC ne sun farmaki ayarin motocin Atiku kan hanyar filin jirgin sama zuwa fadar Shehun Borno.
“An dai samu farmakin ne a wurare guda uku wadanda suka hada da Jagwal kusa da kasuwar wayoyi da ke kan hanyar shataletale na gidan Sir Kashim Ibrahim da kuma na kan hanyar fadar Shehun Borno.”
A bangaren rundunar ‘yansandar Jihar Borno, ta musunta kai hari kan ayarin motocin Atiku a Maiduguri. Kakakin rundunar ‘yansandar Jihar Borno, ASP Kamilu Shatambaya ya bayyana wa manema labarain cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne. Ya siffanta lamarin kai wa Atiku hari mara tushe ballantana makama. Ya ce zargin bai inganta ba kuma yunkuri ne na rusa zaman lafiya a jihar.
Ya ce gangamin ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana karkashin kulawar jami’an tsaro. Ya ce dan takarar shugaban kasan lami lafiya ya isa fadar Shehun Borno bayan ya kammala jawabi ga magoya bayansa a filin taro na Ramat. A cewarsa, Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Abudu Umar yana wurin domin tabbatar da cewa komai ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sai dai, ASP Shatambaya ya ce sun yi nasarar damke wani saurayi mai suna Danladi Abbas dan shekara 32 kan hanyar zuwa filin jirgin sama, bisa jifar ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
“Abbas da wasu ‘yan daba sun yi yunkurin tarwatsa gangamin, amma mun samu nasarar damke daya daga ciki kuma yanzu haka yana hannumu domin gudanar da bincike,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa, tawagar yakin neman zaben Atiku sun sami wasu jerin hare-hare lokacin gangami a Kaduna a ranar 17 ga watan Oktoba. Haka kuma kwanaki kadan bayan wannan, ‘yan daba sun farmaki magoya bayan jam’iyyar a Jihar Zamfara wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da raunata wasu da dama.
Wadannan lamari ba wai a kan jam’iyyar PDP ko Atiku zai tsaya ba, babban barazana ce da za ta iya turnuke zaben 2023, wanda za ta iya hana samun sahihin zabe.
Da take nuna rashin jin dadinta kan rikice-rikice gabanin zabe, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da gargadi kan farmakin magoya bayan jam’iyyu da lalata kayayyakin yakin neman zabe a ko’ina a fadin kasar nan, wanda ta ce hakan bai dace ba kuma ya saba wa dokar zabe.
Akwai bukatar hukumomin tsaro su ja damara wajen kare rayukan mutane da dukkan dan takara na jam’iyyu daga rikice-rikice, domin a samun damar gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Wannan yana da matukar muhimmanci, saboda dukkan zabukan Nijeriya tun daga lokacin da aka samu ‘yancin kai suna gudana ne cikin rikici.
Ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarinsa na tabbatar da ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Duk da jarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takara suka rattaba hannu karkashin kwamitin zaman lafiya da Tsohon Shugaban Kasa, Abdulsalami Abubakar yake jagoranta, akwai bukatar jam’iyyu su cika alkawarin da suka yi na yarjejeniyar zaman lafiya.
NSA Da Babban Sufeta Sun Sha Alwashin Saka Wando Daya Da Gurbatattun ‘Yan Siyasa
Ma’aikatar tsaro ta kasa (NSA) da babban sufetar ‘yansanda na kasa sun sha alwashin saka kafar wando daya da gurbatattun ‘yan siyasa da ‘yan daba da ke kokarin hargitsa harkokin zaben 2023.
Shugaban NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) da Babban Sufeta na kasa, Usman Alkali Baba su suka bayyana hakan a wurin taron shawarwari na hadakan ma’aikatun kan zabe wanda ya gudana a Abuja, inda aka tattauna kan hanyoyin dakile rikice-rikicen zabe.
Monguno ya ce jami’an tsaro suna saka ido kan duk wani mutum ko kungiya da ke kokarin rugutsa harkokin zaben 2023.
Haka kuma, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar da cewa wadanda katun zabensu ya kone sakamakon kone ofishin INEC a karamar hukumar Abeokuta ta kudu a Jihar Ogun za su samu damar yin zabe.
Monguno ya siffanta lamarin da abu mafi muni wanda ba a sake fatan hakan ya faru. Ya ce Shugaba Buhari ya ba shi umurnin gudanar da sintiri a asirce da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2023 cikin lumana.
A nasa bangaren, Usman Alkali Baba ya bayyana cewa ana samun barazana ga zabe tun lokacin da aka fara gudanar da yakin neman zabe. Ya ce hukumarsa ba za ta runtsa ba har sai ta damke wadanda suke da hannu kan lamarin.
Kungiyar Dattawan Arewa Ta ACF Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Rikice-rikice
Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta gargadin ‘yan siyasa kan kalamun batanci da rikice-rikice wajen gudanar da yakin neman zaben 2023.
Kungiyar ta yi wannan gargadin ne a sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi mai taken ‘kalamun batanci da rikice-rikice zai iya kashe mu’. Sanarwar ta samu rattaba hannun sakatare janar na kungiyar ACF, Murtala Aliyu, inda ta bayyana cewa matukar aka kasa daukar mataki kan kalamun batanci da rikice-rikice za su iya wargaza zaben 2023.
Kungiyar ACF ta ce duk da karuwar barazanar tsaro da na tattalin arziki da kasar nan take fuskanta, ‘yan siyasa suna kokarin kunnu da wasu wutan wanda zai kara bai wa rayukan mutane barazana.
“Akwai rahoton da ke cewa wasu ‘yan siyasa suna kokarin hada ‘yan daba domin farmakan abokan hamayyarsu.
“A yanzu haka an fara kalamun batanci da zage-zage a tsakanin ‘yan siyasa ciki har da gwamnoni. Kalamun batanci yana iya janyo tashin hankali mai yawan gaske wanda ya kamata mutane su yi hattara lokacin gudanar da harkokin zabe.”
Gurbatattun ‘Yan Siyasa Na Shirin Amfani Da Ta’addanci Wajen Hargitsa Zaben 2023 — Jega
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa wasu gurbatattun ‘yan siyasa na shirin amfani da ta’addanci wajen hargitsa zaben 2023.
Jega ya kasance mamba a cikin jam’iyyar PRP, ya bayyana hakan ne jam kadan bayan ganawar kwamitin gudanarwa na jam’iyyar domin bayyana manufofinta wanda ya gudana a Abuja.
Ya kara da cewa babbake ofisoshin INEC a wasu sassan kasar nan abun takaici ne, wanda yake nuna cewa wasu gurbatattun ‘yan siyasa na shirin amfani da ta’addanci wajen hargitsa zaben 2023.
“Wannan abun da dukkan ‘yan Nijeriya za su yi adawa da shi ne tare da yin Allah wadai. Abu ne da ya kamata jami’an tsaronmu su hada hannu da karfe wajen aiki kafada da kafada domin damke wadanda suke da hannu kan lamarin tare da daukan matakan da suka kamata domin ganin irin haka bai sake faruwa ba.
“Dole a gudanar da zaben 2023, to ya kamata ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana saboda mu sami jajirtaccen shugaba,” in ji Jega.
Ya yaba wa shugabancin INEC na ganin cewa duk da irin kalubalen da ake fuskanta suna kokarin tabbar da sahihin zabe.
“Duk da dai mun san cewa ‘yan siyasa sun kasance masu zakuwa da suke kokarin rugutsa aiki. Fatanmu shi ne, INEC ta mayar da hankali kan ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a 2023.”