Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da rundunonin ‘yan sanda na jihohin Edo, Delta da Bayelsa sun bayyana cewa sun kammala dukkan wani shiri domin gudanar da manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023 ba tare da wani cikas ba.
Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe na INEC (REC) da ke waɗannan jihohin su ne su ka bayyana haka a hirarrakin da su ka yi a lokuta daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).
A cewar su, ƙarin hare-haren ta’addanci da ake kai ofisoshi da kayan aikin su a faɗin ƙasar nan bai sa sun karaya ba kan ƙudirin su.
Mista Monday Udoh-Tom, wanda shi ne Kwamishinan Zaɓen INEC a Delta, a yayin da ya ke bayyana cewa hukumar ta gama shirya wa zaɓen, ya yi bayanin cewa sun gama dukkan tsare-tsaren da su ka kamata don tabbatar da cewa an yi zaɓe cikin lumana.
Ya ce: ”A cikin watanni takwas da su ka gabata zuwa yau INEC ta yi gagarumin aikin wayar da kan jama’a, domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe sahihi, karɓaɓɓe kuma a cikin adalci.
”Daga cikin ayyukan da hukumar ta gudanar akwai aikin sabunta rajista da kuma karɓar katin shaidar rajistar zaɓe wanda ake kan ci gaba da karɓa a yanzu haka.
Utom ya ce INEC ta riƙa tuntuɓar ƙungiyoyi, hukumomin tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da zaɓe domin zaburarwa zuwa ga gaggauta shirye-shiryen gudanar da zaɓe.
Ya ce INEC ba za ta miƙa wuya ga duk wata barazana ba, don haka sai ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su bai wa hukumar goyon baya domin tabbatar da an yi zaɓe lami lafiya a cikin kwanciyar hankali.
Ba za mu bari a yi cuwa-cuwar cinikin ƙuri’u ba – Rundunar ‘Yan Sanda:
Dangane da irin tanade-tanaden da ta yi a fannin tsaro, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta ce ta daɗe da yin shiri domin ganin cewa an yi zaɓe a cikin kwanciyar hankali a Jihar Edo.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Ɗanƙwara, ya ce sun fito da wani shirin samar da cikakken tsaro, wanda su ka raɗa wa suna ‘Operation Order’, wanda ya ce gaba ɗayan ‘yan sandan jihar kowa na ciki.
Ɗanƙwara wanda Kakakin Yaɗa Labaran ‘yan sandan Edo, Chidi Nwabuizor ya wakilta, ya ce a zaɓen 2023 masu sayen ƙuri’u da dillalan su ba za su ci kasuwa ba.
“Ba za mu gani, ko mu ji labarin ana cuwa-cuwar cinikin ƙuri’u a ranar zaɓe ba,” inji shi.
Su ma kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Delta da Bayelsa sun bayyana irin na su shirye-shiryen da su ka yi, domin tabbatar da samar da tsaro, wanda hakan zai sa a gudanar da zaɓukan 2023 cikin kwanciyar hankali.