ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: INEC Ta Nemi Masu Kada Kuri’a Da Su Duba Sunayensu Cikin Wadanda Ta Yi Wa Rajista

by Sulaiman
3 years ago
INEC

A shirye-shiryen ganin ta gudanar da sahihin zaɓe a 2023, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi kira ga jama’a su yi nazarin jerin sunayen waɗanda ta yi wa rajistar zaɓe domin a tantance yaran da ba su kai shekaru 18 a cikin waɗanda su ka yi rajista ba.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kakakin INEC, Festus Okoye, a wata tattaunawar da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, ranar Litinin.

  • INEC Ta Samar Da Tsarin Yadda ‘Yan Gudun Hijira Za Su Yi Zabe A Zamfara

Ya ce bai yiwuwa a ce babu wasu ‘yan kura-kurai a cikin jerin sunayen waɗanda aka yi wa rajista. “Dalili kenan INEC ke fitar da sunayen a liƙa a faɗin ƙasar nan, domin kowa ya je ya tantance.

ADVERTISEMENT

Okoye ya ce akwai abubuwan dubawa muhimmai guda biyar, waɗanda wajibi ne duk wanda ya yi rajistar shaidar zaɓe, to ya je ya tantance sunan sa.

Bayanai biyar da Okoye ya lissafa, sun haɗa da cewa, ya kamata jama’a su yi wa jerin sunayen rajistar duba na natsuwa, domin su tantance gano yaran da ba su kai shekara 18 ba, domin INEC ta cire su.

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Haka kuma, duk wanda ya yi rajista zai je ya duba da kyau domin ya tabbatar an rubuta sunan sa daidai a rajistar.

Abu na gaba kuma a ya bakin Okoye, ya na da kyau duk wanda ya yi rajista, to ya je ya duba ya tabbatar ba a yi kuskure wajen rubuta duk wasu bayanan da su ka shafe shi ba.

Akwai kuma batun cewa duk wanda ya yi rajista zai je ya duba ya tabbatar cewa hoton sa da aka liƙa, sama bai kalli ƙasa ba.

Batu na biyar kuma shi ne kira ga jama’a su duba domin su taya INEC dubawa da nusasshe ta idan har yanzu akwai sunayen waɗanda su ka rigaya su ka mutu.

Okoye ya ce tuni dai a na ta ɓangaren, INEC ta tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

Sannan ya ƙara da cewa sun bi sunayen dalla-dalla sun cire waɗanda su yi rajista sau biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
Zan Tabbatar Da Bunkasar Harkokin Rayuwar Al’ummar Gombe In Na Zama Gwamna —Hon Keftin Amuga

Zan Tabbatar Da Bunkasar Harkokin Rayuwar Al’ummar Gombe In Na Zama Gwamna —Hon Keftin Amuga

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.