A makonnin da suka gabata ne, dukkan jam’iyyun siyasa 18 da suka fitar da ‘yan takara suka hadu a cibiyar taro kasa da kasa da ke Abuja, domin rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin zabe da kuma bayan zaben 2023.
Duk da dai dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai halarci taron ba, amma mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shettima ya wakilce shi, daga cikin ‘yan takaran har da na babban jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP da na NNPP, Rabiu Kwankwaso da dai sauransu sun rattaba hannun amincewa da ka’idojin kamfen da na zabe.
- Mauludi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 10 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Hutu
- Bai Kamata A Maida Iraki Fagen Takarar Siyasa Tsakanin Bangarori Daban Daban Ba
Kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Abdulsalam Abubakar ne ya shirya taron a matsayin kokari na farko wajen inganta zaman lafiya kafin zabe, yayin da a mataki na biyu kuma ana tsammanin za a kara rattaba hannun a shekara mai zuwa gabanin fara zaben 2023.
An dai gudanar da taron ne kwanaki kadan da kwamitin ya yi ganawa a Minna da ke Jihar Neja, inda Abdulsalam ya bayyana cewa kwamitinsa zai bukaci manyan shugabannin jam’iyyun da su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2023.
A cewarsa, yarjejeniyar zaman lafiyar ba ta takaita ga shugabannin jam’iyyu da ‘yan takara ba ne kadai har da sauran masu ruwa da tsaki da manyan cibiyoyin da ke taka muhimmiyar rawa a cikin zaben kasar nan.
Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan shekarar 1999 da jam’iyyun siyasa guda uku wadanda suka kafa da kafa da juna suka shiga zaben shugaban kasa wanda ake iya tunanin kowa zai iya samun nasara.
Cikin wadannan suka halarci taron rattaba hannun zaman lafiya har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da manyan ‘yan kasuwar Nijeriya da suka hada da Femi Otedola da Aliko Dangote da Sam Amuka da John Cardinal Onayekan da Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN), Prescilla Kuye da dai sauransu, inda shugabanin kasan suka rattaba hannun yarjejeniyar zaman lafiya ba wai kafin zabe ba ko bayan zabe, sai dai domin hatsarin da za a iya fuskanta kan lamarin.
Wannan shi ne karon farko a Nijeriya da ‘yan takarar shugaban kasa da shugabannin jam’iyyun 18 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kundin da aka yi walakabi da “’Yarjejeniyar zaman lafiya na 2022 kan kauce wa rikici da kuma matsalolin yakin neman zaben ga ‘yan takarar shugaban kasa da shugabannin jam’iyyun siyasa da ke takara a 2023.”
Shugaban kwamitin zaman lafiyan, Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa muhimmancin rattaba yarjejeniyar zaman lafiya ga dukkan ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyun siyasa da masu magana da yawunsu mayar da hankali kan ci gaban kasa maimakon hadawa cikin rikici.
Ya kuma yi watsi da labarai da bayanan karya wanda yana daga cikin abun lura a zaben 2023, inda ya ce labarai da bayanan karya ne ke haddasa matsaloli lokacin yakin neman zabe, dole a saka ido wajen kauce kalaman batanci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyu.
Ya ce wannan yarjejeniya zai yi tasiri wajen dakile rikece-rikice da ke tattare da zaben 2023.
Ya kara da cewa ‘yan takaran da jam’iyyun siyasa za su sake rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya a karo na biyu a watan Janairun 2023 kafin ‘yan Nijeriya sukada kuri’unsu a zaben.
Kundin yarjejeniyar yana dauke da yadda ‘yan takara da jam’iyyun siyasa za su yi kokarin gudanar da yakin neman zabe wajen mayar da hankali kan bunkasa manufofinsu, domin tabbatar da cewa magoya bayansu ba su tsunduma wajen janyo rikici ba da saba wa dokokin zabe.
A nasa bangaren a wurin taron, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya yi kira da ‘yan siyasa da jam’iyyu da su gudanar da yakin neman zabensu bisa tsarin doka.
Ya ce a matsayin hukumar zabe na mai kulawa da jam’iyyun siyasa dole ne su saka ido wajen kaucewa duk wani abin da zai tarwatsa zaman lafiyar Nijeriya.
Haka kuma ya ce hukumarsa za ta saka ido kan kudaden da za a kasha lokacin yakin neman zabe kamar yadda doka ta tanada.
A duk shekara kwamitin Abdulsalam ya kan kokarin ganin an rattaba yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ‘yan takara da shugabannin jam’iyya domin kauce wa tayar da yamutsi a lokacin kamfen da kuma lokacin zabe.
Babban abin lura dai shi ne, ko wannan yarjejeniyar zaman lafiya zai iya haifar da da mai ido kamar na 2015?
Alal misali, a zaben 2015 kungiyoyin fararen hula sun bayar da rahoton an samu rikicin zabe guda 61 a jihohi 22, inda aka samu mutuwar mutum 58 a sassa daban-daban na Nijeriya.
A baya dai adadin ya kan zarce hakan, amma sakamakon kwamitin zaman lafiya an samu raguwar lamarin.
Wasu masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa ‘yan siyasa ba sa cika alkawarin da suka rattaba hannu.
Tsohon darakta janar na gidan talabijin na kasa (NTA), Dakta Tony Iredia yana daga cikin wadanda suke ganin ba kasafai ‘yan siyasa suke cika yarjejeniyar da suka rattaba hannu ba.
Ya ce idan aka duba a zabukan jihohin Ekiti da Osun duk da rattaba yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ’yan takara bai hana tashin hankali a tsakanin jam’iyyun da ke hamayya da juna gwabza fada ba.
Ko shakka babu zaben 2023 zai dauki hankali ne tsakanin jam’iyyun APC da PDP da LP da kuma NNPP.
Akwai abubuwa da dama da ke tattare da zaben 2023. Mataki na farko shi ne, INEC ta gudanar da zabe. A mafi yawan lokuta dai INEC ta yi alkawarin cewa ta shirya tsaf wajen gudanar da sahihin zabe.
Hukumar INEC ta ce ta dauki darussa daga zabukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun, inda ta sha alwashin gudanar da sahihin zabe a farkon watanni uku na shekarar 2023.
Idan har INEC ta yi ayyukanta cikin tsari kamar yadda ta yi alkawari, to za asamu karancin rikicin zabe ko kuma ba za a samu rikicin zabe ba kwata-kewata a kasar nan.