Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas, a ranar Juma’a, ta kori ‘yan takara 16 da ke neman kujerun majalisar dokokin jihar a karkashin jam’iyyar APC, daga tsayawa takara a zaben 2023.
Jihar Ribas tana da mazabu 32 inda yankin Ribas ta Gabas ke da rinjaye.
- Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin G20 Da Na APEC Tare Kuma Da Ziyara A Thailand
- Wakilin Sin Ya Bukaci A Kara Kokarin Taimakawa Kasashen Afirka Yakar Ta’addanci
Jam’iyyar PDP ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu mutane 33 a kotu, inda ta nemi a haramta wa ‘yan takarar jam’iyyar APC takara bisa zargin hukumar zaben ba ta sanya ido a zaben jam’iyyarsu ba.
Da yake yanke hukunci a kan kara mai lamba: FHC/PH/CS/152/2022, alkalin kotun, mai shari’a Mohammed Turaki Adamu, ya yanke hukunci a kan wadanda suka shigar da kara.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Andoni, Etche I da II, Tai, Gokana, Oyigbo, Eleme, da Fatakwal I, II da III, Khana I da II Okrika, Ahoada West da Obio/Akpor I da mazabar II.
A halin da ake ciki, shugabancin jam’iyyar APC a jihar ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da kada su yi kasa a gwiwa da hukuncin da babbar kotun tarayyar ta yanke.
Majalisar zartarwa jam’iyyar APC, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawun jam’iyyar, Sogbeye Eli, ta tabbatar da cewa jam’iyyar na yin wani yunkuri na daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A halin da ake ciki, Majalisar zartarwa tana kira ga mambobin jam’iyyar da miliyoyin al’ummar Ribas da ke goyon bayan ‘yan takararmu a mazabar da abin ya shafa da kada su yanke kauna ko kuma su tayar da hankali yayin da muke shirin daukaka kara don sauya hukuncin kotun dom dawo da ‘yan takararmu kafin zabe.
“Idan za a tuna cewa INEC ita ce ta jagoranci tabbatar da cewa ta sanya ido a kan zaben fidda gwanin APC a gaban wani Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal a wani batu da ke kalubalantar cancantar ‘yan takararmu na Majalisar Tarayya.
“Makiyan dimokuradiyya a jiharmu da suke tsoron haduwa da mu a zabe, sun fito ne don karya lagonmu, do tilasta wa ’yan takararmu amma sun kasa.
“Za mu yi takara a zabukan da ke tafe a dukkan matakai kuma za mu yi nasara bayan ajiye wannan hukunci a gefe kamar yadda kundin tsarin mulki ya bai wa jam’iyyar APC dama.”