2023: Kungiyoyi 40 Ke Neman Sanata Yahaya Ya Tsaya Takarar Gwamnan Kebbi

Kebbi

Daga Jamil Gulma,

Samun jagoranci ko kuma wakilci nagari shi ne amfanin zaben wadanda suka kamata saboda haka ne al’umma ke dunkulewa su zabi mutanen da su ke ganin za su iya ba su irin wannan wakilci ko kuma jagoranci.

A tarihin siyasar gundumar Kebbi t a arewa ko jihar Kebbi ko ma Nijeriya ba a taba samun wakilci irin na Sanata Dokta Yahaya Abdullahi Mallamawan Kabi ba wanda har ana ganin ya zarce iyakar aikinsa har ya shiga na kananan hukumomi da gwamnatin jiha.

Wannan shi ne ya sanya wadansu kungiyoyin matasa da na siyasa ke ta kai caffarsu ga Sanata Dokta Yahaya Abdullahi Mallamawan Kabi kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa da ya dawo gida ya ja ragamar mulkin jihar Kebbi saboda suna ganin idan aka yi haka jihar za ta farfado daga halinda ta sami kanta na tabarbarewar arziki wanda a bisa wadansu ma’aunai da a ka dora jihar Kebbi tana daga cikin mafi komabaya daga cikin jihohi har ma daga cikin wadanda aka kirkiro bayanta.

Alhaji Nasco Dakingari shugaba wata kungiyar matasa ne mai magoya baya duk fadin karamar hukumar mulki da Suru wacce tana daga cikin kungiyoyin da suka tabbatarda goyonbayansu ga takarar Sanata Dokta Yahaya Abdullahi idan Allah ya kai mu shekarar 2023.

Ya bayyana cewa a karamar hukumar mulki ta Suru ba su taba sanin suna da wakilci ba sai wannan lokacin, saboda akwai ayukan gunduma da ya kamata a yi musu tun kafin wannan lokacin amma ba su ko taba Jin labarin ayukan ba, misali gine-ginen asibitoci da sanya hasken lantarki mai aiki da hasken rana da sauran ayyuk na hadingwiwa da SDG, akwai kuma samarda magunguna da katan ain asibiti, gina makarantu tare da samarda kayan aiki, samarda ruwan tsaftataccen ruwan sha ta hanyar na’ura mai amfani da hasken rana da kuma lantarki, samarda kayan aikin gona tun kama daga takin zamani na feshi zuwa ainihin takin zamani, injinan banruwa zuwa mashinan kaftu da aka fi sani da suna powertiller, a bangaren samarda ayykan yi kuma an koyawa mata da matasa sama da dubu ashirin sana’o’i tare da ba su jari tun kama daga sana’ar dinki, man shafi, turare, aikin na’ura mai kwakwalwa, babura, KEKE NAPEP da motoci da dai sauransu.

Bayan wannan kuma akwai aiwatar da gyaran tituna tare da shimfida sababbi wanda ba karamar hukumar mulki da ba ta sami wani kaso na tituna ba wanda yanzu haka ana nan ana aiwatarwa.

Wannan shi ne kadan daga cikin dalilan da suka sanya mu ke neman ya dawo ya yi takarar kujerar gwamna a jihar Kebbi.

Mun gani a kasa wanda mafi yawan matasa abinda ya fi daukar hankulansu zuwa ga Mallamawan Kabi shi ne dattako saboda kusan za iya cewa ya cika dukkan alkawurran da ya dauka har ya kara da wadanda al’umma sun cire rai ga samun su musamman ire-iren kananan madatsar ruwa da aka yi a kauyen Bendu da ke karamar hukumar mulki ta Suru wanda ya lakume billiyoyin kudi a wani aiki na hadin gwiwa da ‘ecological funds’.

Exit mobile version