Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce Sanata Ahmed Lawan da Godswill Akpabio ba ‘yan takarar Sanatoci ba ne a mazabar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Hukumar ta ce ba ta amince da ko daya daga cikin ‘yan takarar biyu ba a matsayin dan takarar Sanata a zaben 2023 ba.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Okoye ya ce don tantance gaskiyar hukumar INEC, tun da farko cikakken kwafin takardar tantance zababbun ‘yan takara (Form 9C) da jam’iyyunsu suka daura a Shafin yanar gizo na hukumar a ranar 17 ga Yuni, 2022 lokacin da aka rufe shafin tantance sunayen, hukumar ta shaida wa kowa sunayen ‘yan takarar dake dauke a ciki.