Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RIGAR 'YANCI

2023: MAYAB Ta Sha Alwashin Goyon Bayan Takararar Yahaya Bello

by Muhammad
March 10, 2021
in RIGAR 'YANCI
3 min read
MAYAB
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Awwal Umar,

Kungiyar tabbatar goyon bayan Yahaya Bello a matsayin takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2023 ( MAYAB) ta alwashin ganin za ta tallata manufofinta ga al’umma dan ganin ta jawo gwamnan jihar Kogi yayi takarar shugabancin kasar nan.

Kungiyar mai sunan ” Mobement For The Actualization Of Yahaya Bello For President bisa jagorancin Hon. Muhammad Ubale Marafa tace ta kuduri wannan aniyar ne ganin irin rawar da gwamnan ya taka a jiharsa da ya shafi tsaro da kiwon lafiya, musamman ganin tsayarsa kan rashin kakabawa jiharsa annobar Korona wadda a cewar kungiyar ya zama wani hanyar yin awon gaba da kudaden gwamnati.

Da yake zantawa da manema labarai, a wani taron da kungiyar ta kira a dakin taron sakatariyar hadakar jam’iyyun siyasa ( IPAC) a minna, shugaban kungiyar Hon. Ubale Marafa ya ce, duba da dokar da shugaban kasa ya sanyawa na baiwa masu karancin shekaru damar tsayawa takara, idan ka kwatanta shekarun gwamnan Kogi, Prince Yahaya Bello da rawar da ya taka wajen kawo cigaban jiharsa akwai bukatar al’ummar kasar su jawo shi dan goya mai baya wajen ganin ya mulki kasar nan bayan kammala wa’adin shugaba Muhammadu Buhari.

Da ya juya kan tsarin karba-karba kuwa, Marafa ya ce ba ma goyon bayansa domin tsari ne na ma su son mulkin kasar nan na gudana a tsakaninsu wanda shi ne ya hanawa kasar zuwa inda ya kamata ta kai a yau duk da irin arzikin da Allah ya wadata kasar nan da shi.

Hon. Marafa, ya cigaba da cewar duba irin karfin gaba duk da karancin shekarun sa, Yahaya Bello ya jagoranci sojoji inda ya murkushe ‘yan bindiga mahara da suka zamewa wasu jahobin arewa karfen kafa a yau.

MAYAB ba jam’iyyar siyasa ba ce, kungiya ta masu hangen nesa da suke nazarin yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a kasar nan, ta yi la’akari da yadda duniya tafi mayar da hankali akan matsalar korona fiyeda matsalolin da suka dade suna ciwa al’umma tuwo a kwarya wanda gwamna bai amince da irin wannan siyasar ba duk da cewar idan yana bukatar samun kudi zai bi sahu wajen marawa shirin baya, amma ya zabi kare rayuwar al’ummar jiharsa fiye da tara abin duniya.

Da ya jowa kan matsalar ma’aikatan jihar Kogi na rashin albashi na tsawon watanni, Marafa ya ce wannan matsala da ta shi kusan dukkanin jahohin kasar nan ta hanyar ma’aikatan bugi, wanda sanin kowa ne gwamna Yahaya Bello ya taka mubimmiyar rawa wajen tantance ma’aikatan gaskiya da na bugi da wasu gungun gurbatattun mutane ke anfani da shi wajen yin awon gaba da kudaden gwamnati.

Barista Gambo Gwada, shi ne sakataren kungiyar MAYAB a Neja, ya ce maganar yakin neman zabe, kunguyarsu ba yakin neman zaben Yahaya Bello ta ke yi ba a yanzu, ya ce ba wani dokar kasa da ta bayyana cewar idan wannan shiyyar tayi mulki a baiwa wannan yankin. Mu abinda muke cewa wa yafi cancanta da shugabancin kasar nan idan lokaci yayi bayan shugaba Muhammadu Buhari, sai muka cewar gwamna Yahaya Bello duk da cewar dan yankin arewa ta tsakiya ne yafi cancanta duba da irin nasarorin da ya samarwa jihar Kogi, domin wancan tsarin, tsari ne na jam’iyya da wasu da ke muradin mulki ya dauwama a hannunsu.

Muna da tsarin tafiyar da kungiyar nan daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi, yankuna da jiha kuma kowa ya amince da muradin kungiyar ta hanyar yiwa al’ummar kasa adalci a tafiyar da shugabancin kasar nan ta hanyar baiwa ‘yan kasa ‘yancin zabin shugaban da suke kyautata zaton zai kai kasar ga tudun dafawa.

Hajiya Fatima Maibeza, itace shugabar mata ta kungiyar, tace a tsarin tafiyar da shugabancin kasar nan, ba gwamna da ya nuna adalci a jiharsa kamar yadda gwamnan Kogi yayi duniya ta shaida. Domin shi ne gwamnan da ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar daukar mata a matsayin mataimakansa, haka jami’ar tsaronsa mace ce ya dauka, bayan baiwa mace mukamin shugabar ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, da wasu mukamai da dama.

Saboda mu mata, muna goyon bayan kowace jam’iyya ce za ta amince da baiwa Yahaya Bello takara a zabe mai zuwa mu mara ma ta, amma a yanzu tafiyar mu ba ta jam’iyya ba ce, tafiya ce ta adalci da sanin ya kamata.

A karkashin tafiyar MAYAB, mu mata za mu cigaba da wayar da kan ‘yan mata da matasa wajen muhimmancin yin kira ga gwamna Kogi, Yahaya Bello dan amsa wannan kiran na mu idan lokaci yayi.

MAYAB, dai tace babban abinda ta sanya a gaba shi ne kokarin zakulo nagartattun mutane da zasu jagoranci kasar wajen samar da shugabanci na gari bisa adalci kamar Yahaya Bello dan samun shugabanci na gari ta hanyar samar da tsaro da kare dukiyar kasa.

Saboda shugabancin MAYAB a Neja na kira da babban murya ga gwamna Yahaya Bello da ya karbi wannan kiran hannu biyu dan ceto kasar nan daga halin da ta samu kanta a yau.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ranar Mata: Ya Dace Gwamnatoci Su Sa Ido Ga Matsalolin Mata – Batula

Next Post

Bikin Ranar Mata: Aisha Maikurata Ta Bukaci Mahukunta Su Kara Tallafa Wa Lamuran Mata

RelatedPosts

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Abdullahi Muh’d, Kano Shugaban Gidauniyar ‘Charity’ mai rajin tallafa...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Zubairu M Lawal, A yayin da uwar jam'iyyar APC...

Shafukan

Bagudu Ya Bukaci ’Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa A Shafukan Sada Zumunta

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Umar Faruk, Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, a...

Next Post

Bikin Ranar Mata: Aisha Maikurata Ta Bukaci Mahukunta Su Kara Tallafa Wa Lamuran Mata

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version