Tsohon gwamna Jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce NNPP da LP na tattaunawa kan yiwuwar hadewa don tunkarar zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC.
- Hajjin 2022: Matawalle ya bukaci maniyyata su yi wa Najeriya addu’a ta musamman kan matsalar tsaro
- Machina Ya Yi Barazanar Daukar Matakin Shari’a Kan Sauya Sunansa Da Ahmad Lawan
”Lallai muna tattaunawa saboda ganin cewa PDP da APC babu wanda ya dauki mataimaki daga Yankin Kudu Maso Gabas. A dalilin haka mu ke ganin idan mu ka hade abin zai yi tasiri.
”A cikinmu mutum daya ne zai yi takara daya kuma ya yi mataimaki.”
Sai dai tsohon gwamnan na Kano, bai bayyana wanda zai yi takarar shugaba da mataimaki ba.
”Babba dai babba ne, idan har haɗldewar ta tabbata kowa ya san babba shi ne zai shiga gaba karami kuma ya na biye masa baya. ”
A cewar Kwankwaso jam’iyyun biyu, sun mika sunayen wasu abokan takara na wucin gadi wanda zasu tsaya musu kafin su gama amincewa a tsakaninsu.
”Muna da kwana kusan 40 a nan gaba da zamu ci gaba da tattaunawa a tsakaninmu, domin fito da ainihin sunayen wadanda zasu zama mataimakin shugaban kasa.
“Daga yanzu zuwa kowane lokaci za mu kammala tsare-tsarenmu mu samu matsaya guda daya.”
Tuni mutane da dama suka shiga yin kiraye-kiraye ga tsofaffin gwamnonin biyu kan ganin sun hade waje daya don kawo karshen manyan jam’iyyun biyu na Najeriya, wato APD da PDP.