Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya bayyana cewa idan har za a kayar da jam’iyyar APC a zabe mai zuwa a shekarar 2023, akwai bukatar jam’iyyar PDP ta samu hadin kai a tsakanin ‘ya’yanta.
Da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin Babban Daraktan Save Southern Kaduna Group (SSKG), Mista Istifanus Audu Nimbia da mukarrabansa a wata ziyarar sirri da suka kai, ya bukaci hadin kan ‘ya’yan PDP.
- Badakalar Kudin Makamai: PDP Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Buratai
- Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin
A wata sanarwa daga Mista Victor Mathew Bobai, Daraktan Sadarwa na Save Southern Kaduna Group (SSKG), Sanata Makarfi ya lura cewa, babban kalubalen da ke gaban jam’iyyar PDP a jihar Kaduna shi ne tabbatar da cewa Kudancin Kaduna ya ci gaba da kasancewa tare da goyon bayan takarar Dr John. Ayuba a matsayin abokin takarar wanda zai yi takarar gwamna, Isah Ashiru a zaben 2023.
Makarfi ya ce, “Da farko John Ayuba dan Kudancin Kaduna ne, don haka ‘yan jarida na zuwa suna tada masa hankali ba abu ne da ya dace ba tare da tambayar dan takarar gwamnan PDP matakin tuntubar da ya yi kafin ya isa wurin Dr John Ayuba.”
A cewarsa, ya kamata matasa kada su tada zaune tsaye da neman wasu mukamai masu riba da za su iya gina kwarewa da kuma inganta makomar jihar Kaduna da kasa baki daya.
Ya yi imanin cewa babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da gudummawar da ta dace daga matasa ba.
Tsohon gwamnan ya shawarci matasan da su daina aika sakonnin da ba su dace ba da munanan labaran na nuna kiyayya da yanke kauna, inda ya bukace su da su dauki kansu a matsayin wani bangare na siyasa.
Shugaban na PDP ya ja kunnen matasan da su rika yin tambayoyi kafin su yanke hukunci, inda ya ba su tabbacin cewa kofarsa a bude take a ko da yaushe, suna shirye su zo su yi mu’amala da shi kan batutuwan da ke bukatar karin haske.