Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya karyata rahotonin da ke cewa ya mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi baya a zaben da ke tafe.
Wannan na cikin sanarwar da, Bashir Adefaka ya fitar a ranar Juma’a, insa ya karyata rahoton.
- Bukatar Daukar Mataki Kan Kisan Da ‘Yansanda Ke Wa Fararen Hula
- NIS Reshen Bayelsa Ta Fara Horar Da Jami’anta Kan Tsarin Aiki Da Sarrafa Makamai
Sanarwar ta ce, kwata-kwata irin wannan maganar ma ba za ta fito daga bakin Sarkin ba.
Idan za a tuna dai a ranar Alhamis ne wasu labarai suka karade kafafen sada zumunta cewa Sarkin Musulmi, ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi.
Sai dai a martanin da fadar Sarkin ta fitar, ta nesanta Sarkin daga wannan labari.
“A zahirin gaskiya wannan labarin bai cancanci martaninmu ba, amma kawai don a fayyace komai shi ya sa muke cewa hankali ma ba zai kama wannan batun ba. A matsayinsa na Sarkin Musulmai, Shugaban Majalisar koli na Addinin Musulunci ba zai taba yin irin wannan maganganun ba, don haka jama’a da dama suka sha mamaki tare da shure labarin tun kafin a ce musu karya ce.
“Kuma yana da kyau al’ummar Nijeriya su gane cewa dan takarar LP, Peter Obi gaba daya ma bai ziyarci fadar Sultan a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis ba. Ta yaya har zai furta irin wannan maganganun, hankali ma ba zai kama ba.
“Mun kalubanci masu yada wannan batun da cewa su fito da faifayin bidiyo ko sautin murya na Sultan da ke mara wa Peter Obi baya tare da watsi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu kamar yadda suka nakalto a labarin karyarsu.
Idan ba haka ba, ya kamata su kauce wa shigar da sunan Sultan cikin hidimar siyasa domin wanke sunansa.”
Sanarwar ta ce masu wannan kamfen din ba za su iya karkatar da hankalin Sultan daga ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da ya ke yi a matsayinsa na Sarkin Musulmi ba.