Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Daily Trust ta rawaito cewa, Tinubu ya mika sunan Kabir Masari ne a matsayin wanda zai tsaya gabanin wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ba jam’iyyu na su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023.
- 2023: Ban Ce Zan Dauki Mataimaki Musulmi Ba – Tinubu
- Tun Da Nake Ban Taba Shan Kaye A Zabe Ba – Tinubu
Wasu majiyoyi daga bangaren Tinubu da Masari sun tabbatar wa Daily Trust haka a yammacin ranar Alhamis.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina kuma dan uwan Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina.
Mataimaki na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya taba zama sakataren jin walwala na kasa a jam’iyya APC a lokacin Kwamared Adams Oshiomhole yana matsayin Jam’iyyar na kasa.
Oshiomhole ya shugabanci APC daga 2018 zuwa 2020.
Abokin takarar Tinubu dan jam’iyyar PDP ne a zamanin marigayi shugaba Umaru Musa Yar’adua.
Bayan rasuwar ‘Yar’aduwa a shekarar 2010, Masari ya koma jam’iyyar (CPC), jam’iyyar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara a karkashinta amma ya sha kaye a zaben 2011.
Masari ya yi aiki da shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya hau mulki bayan rasuwar Yar’adua.
Gabanin zaben 2015, CPC ta ruguje tsarinta zuwa APC, Masari ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.
Wasu rahotanni na cewa Tinubu zai maye gurbin Masari kafin zabe saboda yanzu kawai ya mika sunansa ne domin ya cika wa’adin INEC.
“Tinubu yana ci gaba da tuntubar juna kan zabo abokin takararsa. Zai maye gurbin Masari da zarar an zabi wanda ya dace,” inji wata majiya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023,