Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yadawa na cewa yana da niyyar zabar dan uwansa musulmi a matsayin abokin takararsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida yayin taron gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar jiya a Ekiti gabanin zaben gwamnan jihar da ke tafe.
Ya nisanta kansa daga wannan jita-jita, yana mai jaddada cewa yin hakan bai dace da tsarin dimokuradiyya ba, kuma masu yada wannan jita-jitar suna yi ne don kawo masa cikas wajen lashe zaben dake tafe a 2023.
Da dan jarida ya tambaye shi kan shirin sa na zaben mataimakin a takararsa ta shugaban kasa, Tinubu ya amsa da cewa mataimaki na daga yankin Arewa maso Gabas zai futo kuma Kirista ne, duk da cewa har yanzu muna ci gaba da neman shawara kan wanda zamu zaba.